34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Rikici: Gwamnatin Kogi na ƙoƙarin ƙwace kamfanin simintin Ɗangote

LabaraiRikici: Gwamnatin Kogi na ƙoƙarin ƙwace kamfanin simintin Ɗangote

Wani sabon rikici dai ya ɓarke kan mallakin kamfanin simintin Ɗangote tsakanin gwamnatin jihar Kogi da kuma kamfanin wanda yake a garin Obajana, ƙaramar hukumar Kabba jihar Kogi.

Kamfanin ba mallakin Ɗangote bane

Rikicin dai ya samo asali ne sabili da ikirarin da gwamnatin jihar Kogi tayi na cewar kamfanin simintin Ɗangote dake Obajana ba mallakin gamayyar kamfanoni na Ɗangote bane face mallakin gwamantin jihar ta Kogi kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Duk da tarin takardu dake nuni da cewa Aliko Ɗangote ne keda mallakin kamfanin simintin, gwamantin jihar Kogi ta ƙeƙashe ƙasa tace takardun basu cika ƙa’idar samun damar mallakin gurin da kamfanin simintin Ɗangoten yayi ba.

Sai mun amshe ikon gudanarwar kamfanin

Gwamnatin jihar ta Kogi tasha alwashin bin duk wasu matakai wajen ganin ta amshe ikon gudanarwa na wannan kamfani. Haka nan kuma gwamnati tace sai ta karɓi duk wata riba da aka ci tun daga lokacin da aka fara gudanar da kamfanin.

A shekarar 2002 zuwa 2003 ne dai gwamnatin jihar Kogi ta wancan lokacin bisa wata yarjejeniya ta amince da siyar da kamfanin simintin na Obajana zuwa ga gamayyar kamfanoni na Ɗangote wanda ya cigaba da gudanarwa har ya zuwa matakin yanzu.

Majalissa ta bada umarnin rufe kamfanin

Sai dai majalissar jihar Kogi ta wannan lokaci tace bata amince da wancan ƙullin ba. A ‘yan kwanakin nan ne ma majalissar jihar Kogi ta bada umarnin a kulle kamfanin bisa ikirarin da majalissar tayi na cewa babu wasu gamsassun hujjoji dake nuna shedar mallakin gurin.

Majalissar ta hannun kakakinta ta ƙara da cewar ta gayyaci Ɗangote da ya bayyana a gabanta don yazo ya bada bayanin hujjojin da yake dasu kan mallakin gurin da kamfanin simintin Ɗangoten yake gudana, amma bai bayyana a gabanta ba.

Biyo bayan umarnin majalissar, jami’an tsaron sakai na jihar Kogi sun afka ma kamfanin simintin Ɗangoten dake Obajana wanda har hakan yayi sanadiyyar harbe mutane bakwai waɗanda ma’aikata ne a kamfanin.

Ya zuwa yanzu dai, ƙungiyoyi da dama sunyi Allah wadai da abinda gwamantin jihar Kogi ta yi na jibge jami’an tsaron sakai waɗanda suke tada ma al’ummar yankin na Obajana hankali.

A wani labarin na daban, kunji Buhari ya bayyana cewa gwamnatin shi tayi nasarar dakile tashin bamabamai. Shugaba Buhari yace gwamnatin sa tayi gagarumar nasarar daƙile tashin bamabamai a duk faɗin ƙasar nan duk da dai cewa sun gaji matsalar daga gwamnatin data shuɗe.

Yayi wannan ikirari ne a ranar Alhamis a yayin bikin yaye sojoji daga babbar makarantar sojoji ta ƙasa (NDA) dake Kaduna.

Ya kuma zayyano muhimman ayyukan da gwamnatin sa tayi wajen samarwa da jami’an tsaro kayan aiki na zamani masu inganci domin yaƙar ayyukan ta’addanci a faɗin ƙasar.

Shugaban ya ce baya ga sayo kayan aikin da suka dace ga jami’an tsaro, gwamnatin ta shi tayi ƙoƙarin ƙara adadin kuɗaɗe ga manya daga cikin jami’an tsaron.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe