Wasu fastoci guda biyu sun yi kira ga Kiristocin kasar nan da suyi watsi da ‘yan takarar shugaban kasa Musulmai a zaben shekarar 2023 da ke tafe.
Fastocin, Prophet Isa El-Buba fasto David Ayuba, sun ce Kiristocin Najeriya ba su amince da dan Arewa ko Musulmi ya zama shugaban su bayan karewar wa’adin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
Faston baya son dan Arewa ya zama shugaban kasa
Prophet El-Buba, a wajen wani taron addini an jiyo shi yana cewa dan Arewa ba zai taba zama shugaban kasa ga mabiyan sa na wajen taron ba a 2023.
Ni dan Arewa ne kuma mai kishin Arewa. Sannan kuma nace ba dan Arewan da zai zama shugaban kasar ku a 2023. Sannan ba mu yarda wani Musulmi ya zama shugaban kasar mu ba a 2023. Idan kun yarda da abinda nace ku mike kuce amen.
An yi kira ga Kiristoci da su zabi Peter Obi
Fasto Ayuba, a nasa bangaren, yayi kira ga dukkanin Kiristocin Najeriya da su zabi Peter Obi.
Yayi zargin cewa da gangan aka shirya samar da Musulmai a matsayin ‘yan takarar shugaban kasa na manyan jam’iyyun kasar nan. A cewa Ayuba ba wata kabila Hausa-Fulani, saidai kawai Hausa ko Fulani.
Yace:
Manyan jam’iyyun siyasa suna da Musulmai a matsayin ‘yan takarar shugaban kasa ta yadda Kiristoci ba su da wani zabi face su zabi daya daga cikin manyan jam’iyyun.
Ta yadda duk musulmin da ya zo zai cigaba daga inda Buhari ya tsaya. Buhari shine na 16 cikin jerin Musulmai masu karfin fada a ji a duniya. Sun ce Buhari ya taimaki Musulunci sosai. Saboda haka dole shugaban kasa na gaba ya dora daga inda ya tsaya.
2023:Ubangiji ne kadai ya san Waye shugaban kasar Najeriya a zabe mai gabatowa -cewar Fasto Kumuyi
A Wani labarin na daban kuma, fasto Kumuyi yace ubangiji ne kadai ya san waye zai zama shugaban kasa a zaben 2023.
A ci gaba da gabatowan zaben 2023, babban malamin cocin Deeper Life Christian Ministry, Fasto William Kumuyi, ya bayyana cewa Allah ne kadai ya ke da masaniyar waye hugaban kasar Najeriya, inji rahoton The Punch.
Malamin ya bayyana cewa komai yana hannun Allah game da canjin mulki a shekara mai zuwa kuma ‘yan Najeriya za su yi murna da sakamakon.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com