34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Gwamnatin mu tayi nasarar dakile tashin bamabamai – Shugaba Buhari

LabaraiGwamnatin mu tayi nasarar dakile tashin bamabamai - Shugaba Buhari

Shugaba Buhari yace ya gaji matsalar daga gwamnatin baya

Shugaba Buhari yace gwamnatin sa tayi gagarumar nasarar daƙile tashin bamabamai a duk faɗin ƙasar nan duk da dai cewa sun gaji matsalar daga gwamnatin data shuɗe. Yayi wannan ikirari ne a ranar Alhamis a yayin bikin yaye sojoji daga babbar makarantar sojoji ta ƙasa (NDA) dake Kaduna.

Ya kuma zayyano muhimman ayyukan da gwamnatin sa tayi wajen samarwa da jami’an tsaro kayan aiki na zamani masu inganci domin yaƙar ayyukan ta’addanci a faɗin ƙasar kamar yadda the cable ta wallafa.

Shugaban ya ce baya ga sayo kayan aikin da suka dace ga jami’an tsaro, gwamnatin ta shi tayi ƙoƙarin ƙara adadin kuɗaɗe ga manya daga cikin jami’an tsaron.

“A yayin da wannan gwamnati ta karɓi mulki a shekarar 2015, mun karɓi ƙasar ne tana a yamutse, da tashin bamabamai ba ƙaƙƙautawa a manya biranen mu, mun karɓi mulkin kuma mun magance matsalolin.” inji shi.

Mun siyo jiragen yaƙi da dama

“Gwamnatin tamu tayi nasarar siyo jiragen yaƙi na sojojin ruwa aƙalla 550 wanda kuma a yanzu haka guda 319 sun iso. Wannan na cikin shirin da gwamnati take wajen inganta hukumar ta sojojin na ruwa.”

Shugaba Buhari ya ƙara da cewar daga lokacin da suka hau mulki zuwa yanzu, jami’an tsaro sun samu ƙaruwar makamai da ababen hawa na yaƙi kusan aƙalla guda 2000

Shugaban ya kuma yi kira ga shuwagabannin hukumomin tsaro nasa ƙasa, da suyi ƙoƙari wajen ganin sun kawo ƙarshen ta’addancin da ya addabi ƙasar nan kamar yadda suka gama da matsalar a yankin Arewa maso yamma.

Wajibi ne jami’an tsaro su tsare dukiyar ƙasa

Yace wajibi ne jami’an su tashi suyi aiki tuƙuru wajen tabbatar da tsaron dukiyar ƙasa da kuma ‘yan ƙasa baki ɗaya. Yace kada su saki jiki su bar ‘yan ta’adda su lalata dukiyoyi da hanyoyin samun kuɗaɗe na ƙasar.

“A dalilin haka, ina umartar duka shuwagabannin sojojin da suyi aiki tuƙuru irin yadda suka gudanar a Arewa maso gabashin ƙasar nan a guraren dake fama da matsaloli a yanzu, sannan yayi kora ga ɗaukacin ‘yan Nigeria da su cigaba da baiwa jami’an goyon baya da haɗin kai.” inji shugaba Buhari

Shugaban ya kuma jaddada cewa zasu yi iya bakin ƙoƙarin su wajen ganin cewa an gudanar da zabe mai zuwa lami lafiya kuma ba tare da maguɗi ba.

A wani labarin na daban kuma, Harkar Film tayi mun riga da wando – Inji Karima Izzar so. Jaruma Khadija Yobe wacce aka fi sani da Karima Izzar so wacce fitacciyar jaruma ce a masana’antar fina-finai ta Kannywood ta bayyana cewa Film yayi mata komai a duniya nan domin kuwa da shi take ci take sha take gudanar da hidindimunta harma ta taimaki waɗansu.

Jarumar ta bayyana hakan ne a hirar ta da sashin Hausa na BBC a cikin wannan fitaccen shirin nasu na Daga bakin mai ita, wanda yake tattaunawa da wasu shahararrun mutane inda suke bada labarin irin gwagwarmayar da suka sha a rayuwarsu.

Karima Izzar so dai tayi fice ne tunda ta fara fitowa a cikin fitaccen shirin nan mai dogon zango wato Izzar so. Jarumar tayi fina-finai da dama kama daga na bai ɗaya zuwa ga masu dogon zango waɗanda har yanzu ana cigaba da yin wasu daga ciki. Sai dai babu inda jarumar tafi yin suna fiye da Izzar so.

Da aka tambaye ta ko ta yaya ta tsinci kanta a cikin masana’antar Kannywood, Karima Izzar so ta bayyana cewa tun tana yarinya ‘yan film suke burgeta. Bayan data girma, jarumar tace tana tasowa daga Yobe tazo Kano don kallon sabon film idan za’a haska shi a cinema. Ta ƙara da cewa tana son ‘yan film sosai a ranta.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe