31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Namadi Sambo ya fada hannun barayi a Abuja, sun tafka masa gagarumar sata

LabaraiNamadi Sambo ya fada hannun barayi a Abuja, sun tafka masa gagarumar sata

Barayi masu sane sun sace wayar tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo a birnin tarayya Abuja.

An sace wayar tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo ne dai a ranar Alhamis a dakin taro na NAF dake a birnin tarayya Abuja. Jaridar Legit.ng ta rahoto.

An gayyaci Namadi Sambo a matsayin babban bako a wurin taron

Tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo an gayyace shine a matsayin bako na musamman a wurin kaddamar da littafin tarihin Soloman Lar da bude cibiyar shugabanci ta Soloman Lar.

Tsohon sanatan Kaduna ta Arewa Shehu Sani shine ya bayyana labarin satar da aka tafkawa Namadi Sambo a shafin sa Twitter.

Shehu Sani shima yana daya daga cikin bakin da aka gayyata a wurin taron.

Senator Sani ya rubuta cewa:

Abin akwai ban mamaki yadda wani zai iya tsallake tsatstsauran tsaron da aka sanya ya sace wayar tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo a wurin taron dake gudana yanzu haka na kaddamar da littafin Soloman Lar a birnin tarayya Abuja.

An yi wa wani gwamna a Arewa ihu barawo

A Wani labarin na daban Kuma an yiwa wani gwamna a Arewacin Najeriya ihun barawo.

Daruruwan ‘yan jam’iyyar APC sun muzanta  gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq. 

Fusatattun ‘ya’yan jam’iyyar APC, su na shirin sauya sheka zuwa babbar jam’iyyar adawa ta PDP. Amma yayin da Gwamna Abdurrazzaq din ya yi ƙoƙarin shiga tsakani, sai suka kore shi  inda suka dinga  rera taken  “Ole” ma’ana, “barawo” da kuma “Sai Bukky”. 

Taken “Sai Bukky” wani take da ‘yan siyasar jihar Kwara ke yi domin jinjina ga Bukola Saraki, tsohon gwamnan jihar, kuma tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya.

Jihar Kwara na daya daga cikin jihohin da ake ganin rikicin cikin gida na barazana ga jam’iyyar APC mai mulki a daidai lokacin da zaben shekarar  2023 ke kara gabatowa

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe