Ministan watsa labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, yace ba zai taba yiwuwa ba jam’iyyar PDP ta sauya daga dabi’arta ta satar kudaden kasa ba idan har ta sake samun damar komawa kan mulki.
Ministan ya bayyana Hakan ne a yayin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Nigeriya (NAN) a ranar Alhamis a birnin Arusha na kasar Tanzania.
Lai Mohammed na tsokaci ne kan rahotannin da ke cewa wasu daga cikin ‘yan kwamitin gudanarwa na jam’iyyar PDP na kasa sun dawo da N122.4 miliyan da shugaban jami’iyyar ya tura musu. Jaridar Daily Trust ta rahoto.
Akwai rahotannin da ke yawo cewa shugaban jam’iyyar PDP na kasa Iyorchia Ayu, ya biya sama da N100 miliyan ga ‘yan kwamitin bayan kammala zaben fidda gwani na jam’iyyar.
Lai Mohammed yace:
Idan mutum zai iya yiwa kan sa sata, zai yiwa sauran mutane sata ba tare da shakku ba.
Matsalar itace jam’iyyar PDP ba zata taba sauyawa ba, sannan kamar yadda ake cewa ba a sauyawa tuwo suna.
Lokacin da PDP ta Fadi zabe a shekarar 2015, sun amice cewa sun gane kurakuren su, Amma a bayyane yake ba su koyi darasin komai ba.
Allah ya kiyaye, idan har suka sake samun lalitar al’umma, ba za su bar ko Kobo ba.
Mun San abinda muka tarar lokacin da muka amshi mulki a 2015, har yanzu korafi muke akan hakan.
Muna fatan ‘yan Najeriya, yanzu sun ga irin niyyar da suke da ita idan suka karbe madafun iko.
Lai Mohammed ya nemi da PDP da tayi bayanin inda ta samo kudaden
Lai Mohammed yace dole ne a yi wasu tambayoyi kan lamarin ciki har da ko meyasa tunda farko aka biya irin wannan kudin Kuma wannan ne kawai karo na farko.
Ya kuma ce yakamata a tambayi jam’iyyar yadda aka yi ta samo wadannan kudaden.
Lai Mohammed yace a lokacin da yake mamba a kwamitin gudanarwa na ACN da APC, ba kudin da aka biya zuwa asusun sa.
Ban taba tuna cewa wasu irin kudade, kowane iri sun taba shiga asusun Wani mamba na kwamitin gudanarwa na ACN ko APC ba.
2023: Dalilin da yasa PDP zata lashe zaɓen shugaban ƙasa -Atiku Abubakar
Ɗan takarar kujerar shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) a babban zaɓen shekarar 2023, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana cewa jam’iyyar sa zata iya lashe zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.
Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne a jihar Gombe bayan ya ƙaddamar da ofishin yaƙin neman zaɓen sa a jihar
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com