34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Yadda budurwar da bata taba aure ba ta haifi yara 5 a lokaci guda

LabaraiYadda budurwar da bata taba aure ba ta haifi yara 5 a lokaci guda

Oluomachi Linda Nwojo, dalibar ajin karshe a jami’ar noma ta Okpara, Umudike ta haifi yara biyar a lokaci guda dakanta kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Budurwar wacce ‘yar asalin karamar hukumar Ohafia da ke Jihar Abia ce ta haifi yara mata guda uku da kuma maza biyu a ranar Litinin, da misalin karfe 9:02 na dare.

Ta haihu ne a asibitin Tarayya na Umuahia da ke Jihar Abia wanda wannan ne karo na farko da a tarihin asibitin aka taba amsar haihuwar ‘yan hudu.

A wata tattaunawa da wakilin Legit.ng yayi, matar ta bayyana cewa bata taba aure ba. A ranar Talata, wani Prince Krux ya bayyana hotonta da jariran inda yace matarsa ce.

Amma a tattaunawar da wakilin Legit.ng yayi da ita, ta ce bata taba aure ba. Nan da nan mutane su ka dinga tsokaci iri-iri karkashin wallafar: Nkameme Ogechi Caroline tace:

“Wannan kyautar Ubangiji ce. Muna fatan duk idan uban yaran nan yake ya zo ya riki yaran da mahaifiyarsu. Abin ban al’ajabi ne.”

Prince Steven yace:

“Kuma bata taba aure ba? To waye yayi mata cikin? Ya kamata wanda yayi mata wannan aikin ya ci gaba daga inda ya tsaya. Muna mata fatan alkhairi.”

Nkechi Okanu Omorogbe tace:

“Gaskya Ubangiji ya yi mata baiwa. Muna ta samu taimako. Yaran da na haifa guda biyar daban-daban, su ne Ubangiji ya ba wata a lokaci guda.”

Ina jin ƙamshin mutuwa wata bakwai kawai suka rage min” Cewar budurwa cikin kuka

Bidiyon wata budurwa wacce tayi iƙirarin cewa wata bakwai kawai ya rage mata a duniya ya sosa zuƙatan mutane a yanar gizo.

Budurwar mai suna Malkai ta garzaya manhajar TikTok cikin kuka inda ta koka kan yadda ta gaji sannan ta rasa ƙwarin guiwar cigaba da rayuwa.

Ta bayyana cewa tana iyakar bakin ƙoƙarin ta amma abubuwa sun ƙi tafiya daidai. Jaridar Legit.ng ta rahoto.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe