Malam Sabiu, mai sana’ar kaji sannan kuma dilan kai da kafafun kaji ya bayyana irin cuncurindon da mata ke yi a Kano wurin siyan mai da kafafu har da hanjin kaji.
Yayin da wakilin Labarun Hausa ya tattauna da Malam Sabiu, wanda ya kwashe shekaru 12 yana sana’ar ya bayyana yadda mata ke zuwa tun safe neman kai da kafafun kaji.
A cewarsa, an fi cinikin kai da kafafun fiye da asalin kaji don akwai wadanda ke zuwa tun safe har yamma ba su samu ba.
Yana sana’ar tashi ne a kasuwar Tarauni da ke cikin birnin Kano, inda ya shaida yadda musamman mata su ke turo har yaransu don siya saboda rage kwadayi.
Ya bayyana cewa yana samun fiye da N100,000 zuwa N150,000 a ko wacce rana, kuma akwai wadanda ke sara a wurinsu su kara kudi don su siya.
Ya ce yanzu haka ya samu nasarar mallakar gidan kansa kuma yana gab da yin aure don kusan duk shirye-shirye sun kankama.
Bidiyo: Yadda barawon da sace kaji 3 ya boyesu da ransu cikin wandonsa
An yi ram da wani barawon kaji wanda ya rasa inda zai boye su sai cikin wandonsa, LIB ta ruwaito.
Wani mutum dan kasar Ghana ya yi yunkurin boye kajin da ya sace a cikin wandonsa, daga bisani ya sanya wandon don kada a gane shi.
Sai dai buyar bata yuwu ba bayan mutane sun farga inda suka kama shi da kajin dumu-dumu.
Mazauna yankin sun kama shi sannan suka cire kajin daga wandon nasa yayin da suka dinga yi masa bidiyo.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com