Wata fitacciyar mata da ta shahara a Facebook mai suna Jamila Ibrahim ta yi fashin-baki dangane da halin da zawarawa ke shiga bayan mutuwar aurensu.
Ta yi bayani ne a matsayinta na bazawara tare da hasko irin kalubalen da take fuskanta tare da irin kallon da al’umma ke yi musu a wata wallafa da tayi a shafinta na Facebook a ranar 5 ga watan Oktoba.
Kamar yadda ta bayyana, akwai mutane masu gutsiri-tsoma akan zawarawa amma ana rasa wadanda ke tallafa musu da kudi komai kankantarsu.
Ya fara da cewa:
“Wato rayuwar zawarawa gabadaya abin tausayi ne. Idan ku ka rabu da miji ko kuma mijinki ya rasu. Idan iyayenka ba masu kudi ba ne, daga ranar kai za ka yi kanka komai na rayuwa.
“Idan ba ka da sana’a ko aikin yi sai mai imani ne zai iya kama kansa. Shiyasa za ka ga wasu zawarawa na yawon gari wurin bin maza. Da iyaye da ‘yan uwa zasu taimaka da jari da abin zai zo da sauki.”
Ta bayyana yadda wahala ke karuwa idan mata sun rabu da mazajensu yayin da su ke da yara kuma aka sakar musu dawainiyar yaran.
Ta bukaci masu halin taimako da su dinga tallafawa mata idan sun ga sun zo kan yanar gizo su na nema, kowa ta san abinda take ji.
A cewarta, kada mutane su ganta fara kuma da kibarta, ba ta da kudi. Sannan akwai mazan da ba sa auren mace da zarar sun gane tana da yara.
Daga karshe ta roki jama’a da cewa idan ba za su yi musu addu’a ba kada su kashe su don babu macen da za ta rabu da miji idan har yana bata kulawa.
Yadda likitoci suka mayar da wata budurwa abar tausayi bayan ta kashe N60m
Labarin wata ‘yar shekara 18 da haihuwa ya yadu a kafafen sada zumuntar zamani bayan hotunanta sun bazu ta ko ina, shafin Unknown Facts na Facebook ya ruwaito.
Bayan ta je likitoci sun mayar da ita yanayin jarumar turai Angelina Jolie, hakan yasa har aka tura ta gidan kurkuku akan tsoratar da jama’a da tayi da surarta.
Cikin watanni kadan sai da likitoci su ka yi mata aiki sau 50. An haifeta a shekarar 1998, kuma Sarah tana da kyau sosai amma ta nemi sauya halittarta.
Amma tunda likitoci su ka yi mata aiki sai hancinta da lebenta ta koma wata halittar ta daban. An rarake kuncinta sannan an bula mata su har sau biyu.
Burin Sarah shi ne ta bayyana a wata siffa ta daban amma aikin ya mayar da ita abar dariya. Kuma mabiyanta sun dinga mamaki tare da kwasar nishadi.
Sai dai daga baya Sarah ta fara motsa jiki inda ta rame sosai. Hakan yasa mabiyanta su ka dinga caccakarta.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com