Aƙalla mutane 80 ‘yan achaɓa ne rundunar jami’an tsaro na musamman na jihar Ondo suka ce sun kama saboda dalilin rashin bin dokar hana zirga-zirga ga ‘yan achaɓa da aka sanya a jihar.
Gwamnatin Ondo ta hana ‘yan achaɓa aikin dare
A watan daya gabata ne dai gwamnatin jihar ta Ondo ta ƙaƙaba dokar hana zirga-zirga ga ‘yan achaɓa daga ƙarfe shida na yamma zuwa ƙarfe shida na safe (6pm – 6am) a kowace rana. Haka nan jami’an sun haramta ma gidajen casu kaiwa dare da yawa sabili da ba’a yadda wani ya kwana a gidan casu ba.
Vanguard ta wallafa cewa kwamandan rundunar ta Amotekun wato mista Adetunji Adeleye ya zargi ‘yan achaɓa da cewar ayyukan su na ƙara taimakawa wajen ta’azzarar miyagun laifuka a jihar. Ya bayyana hakan ne bayan gudanar da samame kan ‘yan achaɓa a Akure babban birnin jihar.
Aƙalla mutane 80 ne yan kabo-kabo da jami’an na Amotekun suka kama a babban birnin jihar. Shugaban hukumar yace wannan samamen anyi shi ne domin kakkaɓe wasu miyagu masu mummunar manufa akan jihar.

An yadda jami’an tsaro su hau babura
“Mutanen da aka yadda su hau babura da dare sune jami’an tsaro da kuma ma’aikatan dake ayyuka na musamman waɗanda suma dole ne su riƙa yawo da shedar gurin aikin nasu a yayin hawa babur a cikin lokacin dokar.
“Mun fahimci cewa ‘yan achaɓa ne manya masu janyo aikata manyan laifuka a duk faɗin jihar. Saboda haka, zuwa ƙarfe bakwai na yamma mutanen mu zasu koma kan duk wasu mahaɗan hanyoyi da kuma cikin gari don gudanar da aiki.
“Babu maganar hawa babur da dare, duk wanda aka kama yana hawa babur da dare za’a ɗauka cewa ko mai laifi ne kuma za’a ɗauki mataki akan shi daidai da hakan.
An hana zuwa gidan casu da daddare
“Babu maganar zuwa gidan casu da dare, dole ne duk wanda yaje gidan casu ya bar gidan kafin dare ya raba, domin kuwa babu wanda zai ƙara kwana a gidan casu. Mun shirya tsaf wajen ganin mun fatattaki duk wasu nau’o’i na miyagun ayyuka a jihar.” inji kwamandan na Amotekun.
Shin kunji cewa An saki ragowar fasinjojin jirgin ƙasa na hanyar Abuja-Kaduna da aka yi garkuwa da su? A yammacin Laraba ne dai muka samu labarin bkuɓutar ragowar fasinjojin jirgin ƙasa da ‘yan ta’adda suka kwashe a jirgin ƙasa a hanyar Abuja zuwa Kaduna a watan Maris na shekarar 2022.
Jaridar Punch ta wallafa cewa ragowar fasinjojin jirgin ƙasar waɗanda mutum 23 da uku ne sun samu kuɓuta da yammacin yau Laraba da misalin ƙarfe huɗu na yamma (4pm).
Shugaban hukumar tsaron soji ta ƙasa Janar Lucky Irabor ne ya shaidawa manema labarai ta wata takarda batun kuɓutar ragowar fasinjojin jirgin su 23. Ya bayyana cewa jami’an sojoji ne suka yi ƙoƙari wajen samun nasarar kuɓutar da mutanen da suka ɗaɗe a hannun ‘yan ta’addan.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com