34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Sadio Mane yana zuwa taya mu wanke banɗakin masallaci -Limamin Liverpool

LabaraiSadio Mane yana zuwa taya mu wanke banɗakin masallaci -Limamin Liverpool

Shahararren ɗan wasan nan na ƙasar Senegal Sadio Mane ya sha yabo sosai bayan an bayyana wani muhimmin aikin alkhairi da yake yi.

Sadio Mane wanda yanzu haka yana taka leda a ƙungiyar Bayern Munich ta ƙasar Germany bayan ya baro ƙungiyar Liverpool ta ƙasar Ingila, ya samu wannan yabon ne daga limamin wani masallaci a birnin Liverpool.

Limamin masallacin ya bayyana cewa duk da ɗaukaka da tarin dukiya da ɗan’wasan yake da ita, hakan bai hana shi zama mai ƙanƙan da kai ba. Dr Muhammad Salah shine ya bayyana abinda limaimin masallacin ya faɗi game da ɗan wasan a shafin sa na Facebook.

An bayyana wani muhimmin aikin alkhairi da Sadio Mane yake yi

A cewar limamin Sadio Mane yana da tsadaddiyar mota ƙirar Bentley amma idan ya tashi zuwa masallaci bada ita yake zuwa ba.

Ga abinda limamin yake cewa akan Sadio Mane:

“Sadio yana zuwa masallaci a kai a kai, a gidan sa yana da mota ƙirar Bentley,amma yana zuwa wurin mu cikin ƙaramar mota mara tsada. Ba ya fitowa neman suna, kuma baya da girman kai. Har taimakawa yake wurin wanke banɗakin masallacin.

Wannan dai ba shine karo na farko da wani halin kirki na ɗan wasan yake bayyana ba, ko a baya an sha kawo labarai kai abubuwan alkhairi da ɗan wasan yake yiwa al’umma musamman a ƙasar sa ta Senegal.

Ba sa shan giya shi yasa ko da yaushe suke da kuzari, kocin Liverpool ya yabi Mo Salah da Sadio Mane kan rikon su da addini

A wani labarin na daban kuma, mai horas da ƙungiyar Liverpool, Jurgen Klopp ya yabawa Sadio Mane da Mohamed Salah saboda riƙon su da addini.

Mai horas da Liverpool, Jurgen Klopp, ya nuna farin cikin sa cewa taurarin ‘yan wasan sa guda biyu Mo Salah da takwaran sa Sadio Mane su na cikin kuzari da yanayi mai kyau yayin da kulob ɗin ya tunkari wasan shi da kulob ɗin Inter Milan a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai watau Champions  League.

Kocin ya bayyana cewa ‘yan wasan guda biyu su na cikin yanayi mai kyau da kuzari a ko da yaushe saboda ba su shan giya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe