A yammacin yau Laraba ne dai muka samu labarin kuɓutar ragowar fasinjojin jirgin ƙasa da ‘yan ta’adda suka kwashe a jirgin ƙasa a hanyar Abuja zuwa Kaduna a watan Maris na shekarar 2022.
Jaridar Punch ta wallafa cewa ragowar fasinjojin jirgin ƙasar waɗanda mutum 23 da uku ne sun samu kuɓuta da yammacin yau Laraba da misalin ƙarfe huɗu na yamma (4pm).
Duka fasinjojin jirgin ƙasa 23 sun kuɓuta
Shugaban hukumar tsaron soji ta ƙasa Janar Lucky Irabor ne ya shaidawa manema labarai ta wata takarda batun kuɓutar ragowar fasinjojin jirgin su 23. Ya bayyana cewa jami’an sojoji ne suka yi ƙoƙari wajen samun nasarar kuɓutar da mutanen da suka ɗaɗe a hannun ‘yan ta’addan.
Takardar wacce Farfesa Usman Yusuf, shugaban kwamitin tsaron da ya ƙunshi mutane bakwai da suka yi aikin ceto mutanen tana cewa:
“Ina mai farin cikin sanarma ɗaukacin al’ummar ƙasa dama duniya baki ɗaya cewa da misalin ƙarfe 4 na yammacin yau Laraba, 05 ga Oktoba 2022 ne kwamitin mai ɗauke da mutane bakwai da shugaban rundunar tsaro ta ƙasa ya kafa yayi nasarar ceto kafatanin ragowar fasinjojin jirgin ƙasa su 23 da ‘yan ta’addan Boko Haram suka yi garkuwa da su a 28 ga Maris a hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Babu abinda ‘yan ƙasa zasu yi sai godiya
“Babu abinda ‘yan ƙasa zasu yi sai godiya ga shugaban rundunar tsaro ta ƙasa wanda ya tsara gami da ƙaddamar da yadda aka ceto waɗannan mutane tun daga farko har ƙarshe. Sauran ɓangarori na jami’an tsaro tare da haɗin gwuiwar ma’aikatar sufuri sun bada gudunmawa matuƙa wajen aiwatar da aikin.”
Ya ƙara da cewa shugaban ƙasa ya bada goyon baya sosai wajen ganin an kuɓutar da mutanen.
Manbobin kwamitin na godiya bisa wannan dama
“Jajircewa da goyon baya mara iyaka da shugaban ƙasa ya bada ne ya tabbatar da an cimma nasarar aikin.
“Mambobin wannan kwamiti sunyi matukar godiya bisa wannan dama da suka samu ta shiga cikin aikin ceton al’umma. Muna roƙon Allah yayi mana maganin matsalolin mu ya kawo mana zaman lafiya a ƙasar mu baki ɗaya.” inji Farfesa Usman.
A wani labarin, shin kun san yaushe ne bikin Ruƙayya Dawayya da Afakallahu? Batu akan ko yaushe ne bikin jaruma Ruƙayya Umar wacce aka fi sani da Ruƙayya Dawayya, wacce kuma ta kasance mai tsara fina-finai a masana’antar Kannywood da kuma shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, wato Isma’il Na’abba Afakallahu dai abune da mutane da dama suka ƙosa su sani.
Maganar soyayya dai tsakanin jaruma Ruƙayya Dawayya da kuma Isma’il Afakallahu ba wani sabon batu bane, inda duk wani mai bibiyar jarumar a shafukan sada zumunta musamman ma dai na Instagram da Tiktok zai dinga ganin alamun hakan.
Jarumar ta kasance tana yawwa wallafa hotunan Afakallahu, hotunan ‘ya ‘yanshi da kusan duk lamurran da suka shafe shi irin su lamurran siyasa da sauran abubuwa na yau da kullum a shafukan ta na sada zumunta.
Majiyar mu ta mujallar Fim ta bayyana cewa batun soyayya tsakanin Ruƙayya Dawayya da Afakallahu abune da aka ɗaɗe ana gudanar wa cikin sirri. Sai dai abubuwa suka kankama ne jarumar ta fara bayyana wa duniya cewa akwai alaƙa ta soyayya tsakanin ta da shugaban hukumar tace fina-finan.
Shin kuna da wani abin cewa? Za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com