Batu akan ko yaushe ne bikin jaruma Ruƙayya Umar wacce aka fi sani da Ruƙayya Dawayya, wacce kuma ta kasance mai tsara fina-finai a masana’antar Kannywood da kuma shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, wato Isma’il Na’abba Afakallahu dai abune da mutane da dama suka ƙosa su sani.
Soyayya tsakanin Ruƙayya Dawayya da Afakallahu ba baƙon abu bane
Maganar soyayya dai tsakanin jaruma Ruƙayya Dawayya da kuma Isma’il Afakallahu ba wani sabon batu bane, inda duk wani mai bibiyar jarumar a shafukan sada zumunta musamman ma dai na Instagram da Tiktok zai dinga ganin alamun hakan.
Jarumar ta kasance tana yawan wallafa hotunan Afakallahu, hotunan ‘ya ‘yanshi da kusan duk lamurran da suka shafe shi irin su lamurran siyasa da sauran abubuwa na yau da kullum a shafukan ta na sada zumunta.
Majiyar mu ta mujallar Fim ta bayyana cewa batun soyayya tsakanin Ruƙayya Dawayya da Afakallahu abune da aka ɗaɗe ana gudanar wa cikin sirri. Sai dai abubuwa suka kankama ne jarumar ta fara bayyana wa duniya cewa akwai alaƙa ta soyayya tsakanin ta da shugaban hukumar tace fina-finan.

Daga yanzu zuwa kowanne lokaci za’a iya ɗaura auren
Majiyar tamu ta ƙara da cewa ta samu bayanai daga majiya mai ƙarfi kan cewa maganar auren Dawayya ya riga da ya matso sosai. Ana sa ran cewa daga yanzu zuwa kowanne lokaci za’a iya ɗaura auren.
Wasu da Mujallar Fim ɗin ta tattauna da su, sun bayyana cewa akwai yiwuwar ba wani taro za’a yi ba wajen bikin. Sai dai sun bayyana cewa lallai sai sunyi taro, sunyi shagali saboda a cewar su, Dawayya ba ƙaramar mace bace.
Sun ƙara da cewa haɗin Afakallahu da Ruƙayya Dawayya yayi daidai sosai, inda suka ƙara da cewa da zarar sun kammala shirye-shiryen da suke kai a yanzu, zasu bayyana ma jama’a ko yaushe ɗaurin auren ba tare da wani ɓata lokaci ba.
A kwanakin baya-bayan nan ne dai aka ga jarumar ta matsa ƙaimi wajen wallafa hotuna da kuma abubuwan da suka jiɓanci masoyin nata a shafukan sada zumunta musamman ma dai Tiktok da Instagram. A watan Yulin da ya gabata, jarumar ta wallafa wani hoto na Afakallahu haɗe da wani rubutu mai ɗaukar hankali.
Samun Afakallahu Allah ne ya amsa addu’atah
“Samun masoyi na gaskiya a wannan zamanin da rashin gaskiya yayi yawa sai ƙarfin addu’ah. Alhamdulillahi ya rabbi lakal hamdu wash shukur. Allah na gode maka da ka amsa addu’atah. Khairun nasa man yan fa un nass.”

Al’umma da dama a ciki da wajen masana’antar ta Kannywood sun bayyana murnar su sosai akan wannan batu na auren jaruma Ruƙayya Dawayya da kuma Isma’ila Na’abba Afakallahu da ake shirin yi.
A labarin mu na baya, mun kawo muku cewa hukumar zaɓe ta fitar da jerin sunayen ƴan takarar gwamna a zaɓen 2023. Hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta INEC, ta fitar da jerin sunayen ƴan takarar zaɓen 2023 na kujerun gwamna tare dana ƴan majalissun jihohi da zasu fafata a kakar zaɓen dake ta ƙara gabatowa.
Hukumar dai ta fitar da jerin sunayen ne a ranar Talata inda a ciki aka ga cewa sunayen ƴan takarar da suke da rigingimu na cikin jam’iyya, ko kuma batutuwa na shari’a da suke a gaban kotubasu samu damar shiga cikin jerin ƴan takarar na zaɓen 2023 ɗin ba kamar yadda majiyar mu ta Tribune ta wallafa.
Sai dai wannan mataki da hukumar zaɓen ta ɗauka na ƙin sanya sunayen ƴan takara masu rigingimu ya tada ƙura sosai. Wasu magoya bayan su nuna ƙin amincewar su kan wannan mataki na hukumar zaɓen. Idan aka duba za’a ga cewa lokaci yanzu ya kusa ƙure ma ƴan takarar da abin ya shafa.
A jihar Ogun, ƴan takara 13 suka nuna sha’awar neman kujerar gwamna. Sunayen guda 12 daga cikinsu sun shiga cikin jerin da hukumar zaɓe ta fitar. Daga ciki akwai gwamna mai ci kuma ɗan takarar gwamna a jam’iyyar APC wato gwamna Dapo Abiodun.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com