31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Hukumar zaɓe ta fitar da jerin sunayen ƴan takarar gwamna a zaɓen 2023

LabaraiHukumar zaɓe ta fitar da jerin sunayen ƴan takarar gwamna a zaɓen 2023

Hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta wato INEC, ta fitar da jerin sunayen ƴan takarar zaɓen 2023 na kujerun gwamna tare dana ƴan majalissun jihohi da zasu fafata a kakar zaɓen dake ta ƙara gabatowa.

Banda waɗanda ke kotu a jerin na zaɓen 2023

Hukumar dai ta fitar da jerin sunayen ne a ranar Talata inda a ciki aka ga cewa sunayen ƴan takarar da suke da rigingimu na cikin jam’iyya, ko kuma batutuwa na shari’a da suke a gaban kotubasu samu damar shiga cikin jerin ƴan takarar na zaɓen 2023 ɗin ba kamar yadda majiyar mu ta Tribune ta wallafa.

Sai dai wannan mataki da hukumar zaɓen ta ɗauka na ƙin sanya sunayen ƴan takara masu rigingimu ya tada ƙura sosai. Wasu magoya bayan su nuna ƙin amincewar su kan wannan mataki na hukumar zaɓen. Idan aka duba za’a ga cewa lokaci yanzu ya kusa ƙure ma ƴan takarar da abin ya shafa.

A jihar Ogun, ƴan takara 13 suka nuna sha’awar neman kujerar gwamna. Sunayen guda 12 daga cikinsu sun shiga cikin jerin da hukumar zaɓe ta fitar. Daga ciki akwai gwamna mai ci kuma ɗan takarar gwamna a jam’iyyar APC wato gwamna Dapo Abiodun.

Bayan nan akwai Biyi Otegbeye na jam’iyyar ADC, Omosanya Monsuru a jam’iyyar Accord, Adeyemi Olufemi na AA, Harrison Adeyemi na jam’iyyar AAC, Sokunbi Olanrewaju a ADP, Jolaoluwa Emmanuel na APM, Falana Omoshile a APP, Oguntoyinbo Ajadi a jam’iyyar NNPP, Ogunronmbi Oludayo na NRM, Bamgbose Olufemi na PRP da kuma Ojesina Anthony na jam’iyyar SDP ne suka samu damar shiga jerin ƴan takarar gwamna na zaɓen 2023 a Ogun.

A satin daya gabata ne dai, wata babbar kotun gwamnatin tarayya dake zamanta a Abuja ta yanke hukunci kan koken da wasu ƴaƴan jam’iyyar PDP na jihar Ogun su uku suka shigar. Sun yi ƙorafin ne kan sunayen delegate s da aka yi amfani dasu a yayin gudanar da zaɓen fitar da gwani.

Sunan kowa ya fito a jihar Jigawa


A jihar Jigawa, hukumar zaɓe ta tantace duka ƴa takarar gwamna na jam’iyyu 11 da suka sayi tikiti, ta kuma basu damar fafatawa a kakar zaɓen 2023 mai zuwa. A ciki akwai mataimakin gwamna mai ci na yanzu Malam Umar Namadi na APC, sannan akwai Alhaji Mustapha Sule Lamido na jam’iyyar PDP, sai kuma Alhaji Ibrahim Aminu Ringim na NNPP.

A jihar Ebonyi kuwa, kakakin majalisar jihar mai suna honorabul Ogbonnaya Nwifuru na jam’iyyar APC, da kuma Ifeanyichukwuma Odii a jam’iyyar PDP na daga ƴan takarar da zasu fafata a kakar zaɓen 2023 a jihar.

Sauran sun haɗa da Opoke Sunday a jam’iyyar YPP, Usulor Anthony a NRM, sannan sai Chukwuma Nwandugo a AA da dai sauransu.

A jihar Oyo, gwamna mai ci wato gwamna Seyi Makinde ne na jam’iyyar PDP ne zai kara da ƴan takara 15 na sauran jam’iyyu a kakar zaɓen na 2023 mai zuwa.

A jihar Kwara kuma, hukumar zaɓen ta fitar da sunayen ƴan takara ne daga jam’iyyu 14 waɗanda ke neman kujerar gwamna a jihar. Gwamna mai ci a yanzu Abdulrahman Abdulrazaq da mataimakin sa, Kayode Alabi, sune ƴan takarar a jam’iyyar APC, a sa’ilin da Abdullahi Yaman da kuma Makanjuola Gbenga ne halastattun ƴan takara PDP a jihar.

Tsohon shugaban jami’ar Ilorin UI wato Farfesa Abdulraheem Shuaib Oba shine ɗan takarar gwamna na NNPP a jihar ta Kwara. Sauran jam’iyyun dake da ƴan takara sune ZLP, AA, AAC, ADC, ADP, APM, APP, LP, PRP, SDP, da kuma YPP.

INEC ta bayyana sunayen wasu duk da suna Kotu

A jihar Taraba kuma, duk da kasancewar akwai shari’a a gaban kotu kan wasu ƴan takarar, hukumar zaɓen ta bayyana sunayen su cikin jerin waɗanda za’a fafata dasu a zaɓen 2023.

A wani labarin na daban kuma, mawaƙin Najeriya ya je taro Turai da bunsuru don ya nishadantar, bunsurun ya dinga dabbanci.

Mawakin Najeriya, Asake ya yi fice akan dadin muryarsa a duk lokacin da yayi waka, kuma a wannan karon da yaje Atlanta don yin waka ya je wa da masoyansa da tsaraba.

Yanzu haka mawakin yana Amurka sannan ya bayyana gaban jama’a da abinda ba su taba tunanin zai je dashi ba. Kafin ya fara wakar, sai ga shi da bunsuru daure da igiyarsa wanda hakan ya yi matukar nishadantar da turawan da su ke je wurin.

Sai dai bunsurun nan ya ki tsayawa dakyau duk da yana daure da igiya amma ya gaza bai wa Asake hadin kai don yayi wakarsa ya kammala lafiya.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da saƙo ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe