Wata mata ta bayyana wa duniya hoton gadon da ta siya a shafinta na Twitter, @LeratoRSA, inda tace ta wahala a shekarar nan ta sha wahala mai yawa, Legit.ng ta ruwaito.
Ta bayyana yadda ta kwashe watanni biyar tana bacci a kasa kafin Ubangiji ya azurta ta da kudi ta siya gado mai kyau. Nan da nan mutane su ka dinga yi mata fatan alkhairi ta hanyar tura mata sakwanni su na taya ta murna. Kamar yadda ta bayyana a shafinta:
“Na wahala kwarai a wannan shekarar, amma na samu haske a wannan gabar.”
‘Yan Najeriya da dama sun dinga cewa gadaje masu kyau ba su da arha a zamanin nan. Mu na taya ta murna ganin cewa ta wahala da farko amma yanzu ta samu sauya mai kyau.
Tsokacin jama’a karkashin wallafar tata:
@Current2620 yace:
“Lalela wannan ai babbar nasara ce. Kiji dadinki. Komai kankantar nasararka ya kamata kayi murna akanta. Kiyi bacci mai kyau ‘yar uwa.”
@Cleeeyo_ yace:
“Gaskiya babbar nasara ce a gare ni, in samu aiki har in siyawa kaina gado.”
@ChifChiduku yace:
“Ya kamata ayi murna akan nasara komai kankantarta.”
“Ngiyakubongela cc tace:
“Wannan ya sa min kwarin gwiwa. Nagode.”
A gado daya muke kwana: Yadda tagwaye su ka dirka wa mace daya ciki, tana gab da haihuwa
Wasu tagwaye sun janyo cece-kuce bayan sun bayyana yadda su ke kwanciya da mace daya kuma yanzu haka su na shirin tarbar jaririnsu don ta kusa haihuwa, Legit.ng ta ruwaito.
A gado daya su ke kwana kullum kamar yadda su ka bayyana. Kuma wannan lamarin ne yafi bai wa kowa mamaki.
A wani bidiyo da Nicholas Kioko ya saki a shafinsa ba Youtube, tagwayen sun bayyana irin rayuwar soyayyar da su ke yi da matarsu.
Teddy da Peter sun bayyana cewa su na gab da zama iyaye kuma ba su riga sun yi aure ba tukunna amma su na kiranta da matarsu.
Kamar yadda Teddy yace:
“Mu da matarmu ne muka zama. Kuma mun yanke shawarar aurenta ne kasancewar mu tagwaye. Yanzu haka a daki daya muke kwana.”
Sun bayyana yadda su ka hadu a coci wanda daga nan ne su ka yi musayar lambar waya da ita.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com