34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Mawakin Najeriya ya je taro Turai da bunsuru don ya nishadantar, bunsurun ya dinga dabbanci

LabaraiMawakin Najeriya ya je taro Turai da bunsuru don ya nishadantar, bunsurun ya dinga dabbanci

Mawakin Najeriya, Asake ya yi fice akan dadin muryarsa a duk lokacin da yayi waka, kuma a wannan karon da yaje Atlanta don yin waka ya je wa da masoyansa da tsaraba, Legit.ng ta ruwaito.

Yanzu haka mawakin yana Amurka sannan ya bayyana gaban jama’a da abinda ba su taba tunanin zai je dashi ba. Kafin ya fara wakar, sai ga shi da bunsuru daure da igiyarsa wanda hakan ya yi matukar nishadantar da turawan da su ke je wurin.

Sai dai bunsurun nan ya ki tsayawa dakyau duk da yana daure da igiya amma ya gaza bai wa Asake hadin kai don yayi wakarsa ya kammala lafiya.

A bidiyon da ya dinga yawo a kafafen sada zumuntar zamani, an ga yadda Asake ke jan bunsurun da karfi shi kuma dabban yana fincikar kansa.

Ga bidiyon:

Mutane sun yi tsokaci iri-iri:

wunmimarin tace:

Ya san yadda bunsuru ke da taurin kai, babu yadda za ayi ya natsu.

sari_supergal tace:

Masu rajin kare kare hakkin dabbobi za su nemo ka.”

vikyornjoku yace:

Da fatan asalin mai kiwon dabban yana kusa. Idan bunsurun yayi yunkurin tserewa.“

An chafke mawaki Ice Prince da laifin guduwa da Dan Sanda

An kama mawakin rapa na Najeriya, Panshak Henry Zamani, wanda aka fi sani da Ice Prince Zamani, bisa zarginsa da sace wani dan sanda.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a safiyar Juma’a inda ya bayyana yadda aka kama mawakin.

Ya ce an kama mawakin ne da laifin cin zarafin wani dan sanda da ya hana shi tukin mota ba tare da lasisi ba.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Mista Hudenyin ya yi zargin cewa mawakin ya yi barazanar jefa jami’in cikin kogi a daidai lokacin da aka kama shi.

Jami’in ya saka hoton mawakin a daure inda ya ce za a tuhume shi.

“Da karfe 3 na safiyar yau an kama @Iceprincezamani a dalilin tukin mota ba tare da lasisi ba. Ya amince a kai shi ofishin yan sanda. Daga haka ne ya yi awon gaba da dan sandan da ke cikin motarsa, inda ya yi masa barazanar jefa shi a cikin kogi. An kama shi kuma za a gurfanar da shi a gaban kuliya”.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe