Ƴan sanda a jihar Ekiti sun cafke wani ɓarawo Akindele Opeyemi Olugemi mai shekara 32 wanda ya sace kuɗaɗen sadakar da aka tara a wata cocin jihar.
Wanda ake zargin yana tafiya ne a kan babur ɗauke da jaka lokacin da aka tsayar da shi domin a duba shi. Da farko ya ƙi yarda a binciki abinda yake ɗauke da shi amma daga ƙarshe ƴan sanda sun yi masa ta ƙarfi. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.
Bayan an yi masa binciken ƙwaƙwaf, an samu ƙuɗaɗe a tattare da shi. Ko da aka masa tambayoyi bai bayar da gamsashshiyar amsa kan yadda ya samu kuɗin ba.
Binciken ƴan sanda daga baya ya gano cewa ya sato kuɗin ne daga cocin Christ Apostolic Church, Camp Ground a Ikeji, Ara-Ikeji, jihar Osun.
Ya amsa laifin da ƴan sanda ke tuhumar sa da shi, inda yace yayi aiki a matsayin mai gadi a cocin na tsawon shekara biyu, sannan yayi murabus a farkon shekarar nan.
Yadda ɓarawon ya sace kuɗaɗen
Yayi basaja ya koma cocin domin yin addu’a cikin dare inda daga bisani ya lallaɓa ya je wurin ajiye kuɗin cocin yayi awon gaba da su.
Ko da aka ƙirga kuɗaɗen adadin su ya kai Naira dubu ɗari shida da ɗari ɗaya da sha biyar (N600,115)
Ƴan sanda sun bayyana cewa za a tura wanda ake zargin zuwa kotu tare da sauran masu aikata laifuka da hukumar ta tasa ƙeyar su a jihar.
Wata budurwa mai rawar TikTok a masallaci ta faɗa komar ƴan sanda
A wani labarin na daban kuma, ƴan sanda sun cafke wata budurwa mai rawar TikTok a masallaci.
Ƴan sanda a birnin Islamabad na ƙasar Pakistan sun cafke wata budurwa mai amfani da manhajar TikTok bisa laifin tiƙar rawa a masallaci.
An kama budurwar ne tare da ƴan tawagarta a ranar Litinin bayan bidiyonta tana rawa a masallacin Faisal ya ƙaraɗe shafukan sada zumunta
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com