31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Zama da saurayina a gidan mijina ya sanya musu shakuwa mai yawa, Matar aure

LabaraiZama da saurayina a gidan mijina ya sanya musu shakuwa mai yawa, Matar aure

Tamica Wilder wata mata ce da ke zama a gida daya da saurayinta da kuma mijinta tare da yaranta, Legit.ng ta ruwaito. Tamica ta hadu da mijinta tun shekaru sha-daya da su ka gabata, kuma ta sanar da shi cewa ba ta niyyar zama da shi, shi daya.

Kamar yadda New York Post ta nuna, tana son soyayya da maza da dama a lokaci guda, a lokacin da ta sanar da shi bai fahimta ba, amma yanzu ya gane. Tamica ta bayyana yadda mijinta da saurayinta su ka shaku da juna kwarai bayan barinsu su yi alaka da juna.

Bayan haihuwar yaranta biyu, bayan shekaru 11 da haduwarta da mijinta, ta hadu da wani masoyin yayin wani biki da taje. Bayan komawarta gida ta sanar da mijinta labarin sabon saurayin nata kuma ta ce ba ta son rabuwa da shi.

Ba na da burin kin sake ganinsa. Akwai wani abu da nake ji a jikina dangane da shi kuma soyayya ce wacce ba zan iya kyaleta ba,” a cewarta.

Ta ci gaba da haduwa da saurayin wanda daga bisani ta dawo da shi gidan mijinta inda tace alakarsu ta kara karfi bayan cudanyar da yake yi da yaranta. Shakuwarsu ta kai ga har su na fita yawon shakatawa da mijinta tare da shi.

Hakan yasa yaranta ke masa kallon uba saboda yana matukar wasanni da su, ya taya su aiki tare da cin abinci dasu.

Budurwa ta kunshi takaici bayan raka kawarta da saurayi wurin cin abinci, ya ki siya mata komai

Samari da dama sun yaba wa wani matashi wanda ya dauki wani tsatstsauran mataki akan kawar budurwarsa bayan ta raka budurwar tare da shi wurin cin abinci, Legit.ng ta ruwaito.

Mutumin ya ki siya wa kawar komai a bidiyon kuma ya nuna halin ko in kula duk da dai bidiyon ya nuna yadda kawar ta shiga damuwa. Nan da nan aka dinga yada bidiyon wanda aka ganshi da budurwarsa su na morar abincinsu yayin da ita kuma kawarta ke zaune babu komai a gabanta. Wanda ya wallafa bidiyon a TikTok har zolayar kawar yayi wacce aka ganta zaune cike da damuwa. Har yana cewa sai da aka ja kunnen kawarta akan kada ta kuskura ta je da kowa. A bidiyon, an lura da yadda matashin ke morar abincinsa shi da budurwarsa yayin da ta gefensu ke zaune cike da damuwa. Mutane da dama sun yi ta caccakar budurwar akan yadda ta bari har saurayinta ta tozarta mata kawa, yayin da maza su ka dinga yaba wa saurayin akan share kawar budurwarsa da yayi.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe