Gwamnatin tarayya ta fara bin hanyar soke rajistar ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa (ASUU).
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ƙungiyar Congress of Nigerian University Academics (CONUA), wani ɓangaren ASUU da ya ɓalle, ta samu rajista a hukumance a matsayin ƙungiyar ma’aikata.
Wata majiya a ministirin kwadago da samar da aikin yi, ya tabbatarwa wakilin jaridar Daily Trust cewa ministan kwadago, Chris Ngigie, zai miƙa katin shaidar rajista ga sabuwar ƙungiyar kafin wucewar ranar yau.
Majiyar ta yi bayanin cewa wannan ƙoƙarin na gwamnatin tarayya na daga cikin hanyoyin da take bi domin soke rajistar ASUU, domin magance yawan tafiya yajin aikin da ƙungiyar ke yi wanda ya durƙusar da karatu a jami’o’in gwamnati har na tsawon watanni bakwai.
Minista Chris Ngige, a madadin gwamnatin tarayya zai miƙa katin shaidar rajista a yau ga ƙungiyar Congress of Nigerian University Academics (CONUA). Da wannan, akwai yiwuwar a shafe tarihin ASUU a cikin jami’o’in mu.
A cewar majiyar
A watan Satumba gwamnatin tarayya tayi barazanar janye rajistar ASUU a matsayin ƙungiyar ma’aikata bisa zargin da ake mata na kasa miƙa yadda ta kashe kuɗaɗen asusunta na shekara biyar da suka gabata.
Rajistaran ƙungiyoyin ma’aikata har takardar gayyatar zuwa kare kai ya turawa ASUU kan ko a wane dalili zai hana a soke takardar shaidar rajistar ta bisa yiwa doka karan tsaye.
Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari
A wani labarin na daban kuma, shugaba Buhari yace yajin aikin da ASUU ke yi na matuƙar sosa masa rai.
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin raɗaɗin zafin cigaba da yawaitar samun tsaikon da ɓangaren ilmin gaba da sakandire ke samu a ƙasar nan.
Haka kuma shugaba Buhari yayi kira ga ƙungiyar malaman jami’a ASUU da ta janye yajin aikin ta na wata bakwai, sannan a buɗe makarantu yayin da ake cigaba da tattaunawa don ganin an biya musu buƙatun da ba su fi ƙarfin gwamnati ba
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com