Kabilar Bodi ko Me’en su na rububin maza masu katon tumbi. Su na zaune ne a yankin tafkin Omo da ke Ethopia kuma babban abin burgewa dangane da kabilar shi ne yadda mazansu ke shan jini da madarar shanunsu don suyi kiba, Nigerian Pulse ta ruwaito.
Yayin da ake saura watanni shida ayi gasar neman aure, iyayen za su zabi namiji guda wanda zasu shirya don shiga gasar. Yana tafiya ne wata bukka inda zan dinga shan jini da kuma madarar shanu, sannan ba zai kusanci ko wacce mace ba yayin shirin.
Da garjin rana zai yi sauri yasha jinin yadda zai shiga jikinsa da kyau, amma sakamakon kyankyani, akwai mazan da su ke yin amai. Bayan watanni shida da fara shan jinin, mazan za su fito don kowa ya nuna katon cikinsa kuma daga nan za a dauke su a jarumai har karshen rayuwar su.
A ranar gasar, mazajen za su nuna cikinsu wanda za su shafe shi da toka da kasa. Akwai mazan da tsabar kibar da su ke yi ko tafiya ba sa iyawa dakyau. Bayan sun shafe jikinsu da kasa da toka su na fitowa ne daga bukkokinsu inda za a fara gasar.
Su na zagaye wata bishiya ne yayi da mata ke basu giya su na kambama su su kuma su na sharbar zufa. Duk namijin da yafi sauri yayin zagayen ne za a zaba sannan za a yanke sa.
Bayan kammala shagalin zai dage wurin sabe kibar da yayi don ci gaba da rayuwarsa ta yau da kullum. Sai dai ko wanne namijin yana da burin kasancewar namijin da yafi kowa kiba.
Maasai: Kabilar da ake tofa wa amarya ‘Miyau’ a matsayin hanyar sanya wa aurenta albarka
Yayin da wasu kabilun duniya ke kallon tofa miyau a matsayin hanyar rashin kunya da cin mutuncin jama’a, kabilar Maasai da ke Kenya da arewacin Tanzania na kallon hakan a matsayin hanyar mutuntawa da sanya albarka, Nigerian Pulse ta ruwaito.
Kabilar Maasai kaso 1 ce bisa 100 na mutanen Kenya da arewacin Tanzania, amma an san su da dabbaka al’adunsu tsawon lokaci wadanda su ka bambanta da na sauran jama’a.
An san su da daukar hankula, hakan ya sanya jama’a ke zuwa yankinsu don yawon bude ido, sai kuma sutturunsu na daban ne.
Su na amfani da Shuka, wani yadi mai kalar ja, tare da duwatsu masu ban sha’awa a wuya da hannayensu. Sai dai ba wannan bane abin daukar hankali face al’adarsu ta tofa miyau.
Ba kamar sauran al’adun duniya ba, Maasai ba sa jin haushi don mutum ya tofa musu miyau, a wurinsu albarka ya sanya musu tare da fatan alheri.
Misali, Maasai su na tofin miyau a hannu kafin su gaisa da jama’a a matsayin hanyar mutuntawa da kuma girmamawa, duk da ba kowa ake yi wa hakan ba.
Idan kuwa aka yi maka hakan ka tabbatar kai din mai sa’a ne kuma mai daraja.
Maasai su na tofa wa jarirai miyau don yi musu fatan tsawon rai da samun nasarorin rayuwa. Ba iyayen jariran kadai ke tofa musu miyau ba, har da sauran ‘yan uwa da abokan arziki.
Wasu sun yarda da cewa tofa wa jarirai miyau na iya wanke musu zunubbansu.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausa.com