31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Magidanci yace ga garin ku nan bayan ya kwankwaɗe kwalaben burkutu

LabaraiMagidanci yace ga garin ku nan bayan ya kwankwaɗe kwalaben burkutu

Wani magidanci da ba a san kowane ne ba wanda yayi kurin cewa zai iya shanye kwalba sha ɗaya na burkutu ba tare da yayi marisa ba, ya sheƙa barzahu bayan ya kwankwaɗe su.

Mutumin dai ya fito ne daga ƙaramar hukumar Bokkos ta jihar Filato.

Ya bugi kirjin cewa zai shanye kwalba 11 na burkutu

Hafsat Abubakar ta ƙungiyar ‘Women Leaders of the Conflict Mediation Mitigation Regional Council’, reshen jihar Filato, tace magidanci ya buƙaci da mai siyar da burkutun ta bashi kwalba 11 sannan ya rantse cewa zai gama da su ba tare da wani abu ya faru da shi ba.

Hafsat Abubakar, wacce ta samu labarin abinda ya faru a mashayar, ta gayawa jaridar Legit.ng cewa magidancin ya samu nasarar shanye kwalba tara amma ya kasa cigaba da kwankwaɗe sauran kwalba biyun.

Nan take yace ga garin ku nan

Tace nan take magidancin ya mutu yayin da mai siyar da burkutun ta tattara kayanta ta ranta a na kare

A cewar ta, kafin mutuwar magidancin, ya riƙa aman jini ba ƙaƙƙautawa ta hanci, kunne da baki.

Ta kuma ƙara bayyana cewa wani mafarauci ne wanda ya zo wucewa ya ga gawar mutumin sannan ya ankarar da mutanen ƙauyen suka binne shi.

Mamacin yana da matar aure ɗaya da ƴaƴa biyar.

Hisbah a Zamfara ta fashe giya da ta kai ta Naira miliyan 50

A wani labarin na daban kuma, hukumar Hisbah ta fashe giya da ta kai ta Naira miliyan hamsin a jihar Zamfara.

Hukumar hisbah a Zamfara ta bayyana cewa sunyi nasarar kame tare da fashe kwalebanin giya da suka kai na kimanin kuɗi har Naira miliyan 50 a jihar.

Hakanan hukumar ta sanar da rufe wani shahararren otal mai suna ‘Top town hotel’ wanda yake a Igala kwatas dake cikin Gusau babban birnin jihar ta Zamfara.

Da yake jawabi a ranar Lahadi yayin gabatar da jawabi tare da bayyana waɗanda aka kama dangane da hakan tare da nuna nau’o’in giya daban-daban da aka kama, Kwamishinan dake kula da zangon wato Usman Buhari Maijega, ya bayyana cewa sun kulle wani shahararren katafaren otal

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe