31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Wutar rikici ta kunno tsakanin Rahama Sadau da Mansurah Isa

LabaraiKannywoodWutar rikici ta kunno tsakanin Rahama Sadau da Mansurah Isa

Cece-kuce ya ɓarke a tsakanin jaruma Rahama Sadau da Mansurah Isa akan sunayen ƴan kwamitin mata na yaƙin neman zaɓen Tinubu.

A cikin jerin sunayen akwai jarumai mata 33 daga masana’antun finafinai na Nollywood da Kannywood.

Sai dai, jerin sunayen ya ƙunshi sunan Rahama Sadau. A wani martani da tayi a shafin Twitter, jarumar ta nesanta kanta da jerin sunayen, inda tace tsantsagwaron ƙarya ce.

Wasu jaruman da suke a cikin jerin sunayen sun haɗa da Joke Silva, Mansurah Isah, Fausat Balogun, Remi Oshodi, Mercy Johnson, Rose Odika, Sola Kosoko, Lanre Hassan (Iya Awero), Hajiya Nas, Lizzy Jay (Omo Ibadan), Princess Kalihat Bello, da sauran su.

Mansura Isah ta yiwa Rahama Sadau raddi

DJaridar Daily Trust ta ambato Mansurah Isa na martani a kan maganar da Rahama Sadau tayi, Mansurah Isa, wacce ita ma tana cikin ƴan kwamitin, a wani rubutu a shafin ta na Instagram, tace duk da hoton Rahama ya fito a cikin sunayen, ba sunan ta ake nufi na wata jarumar kannywood ce Rahama MK ba Rahama Sadau ba.

A kalaman ta:

Zuwa ga Rahama, sunan da kika gani a cikin jerin sunayen ba sunan ki bane tun asali. Sunan Rahama MK ne sannan tun da sun san ki kawai a Rahama daga Kannywood, sai suka yi zaton cewa ke ɗin ce. Amma kada ki damu, ba ke ake nufi ba.

Rahama Sadau ta mayar da martani

Da take martani kan maganar da Mansurah tayi, Sadau tayi nuni da cewa na gaba da ita sun kira ta sun ba ta haƙuri kan tuntuɓen da aka samu.

Sadau ta rubuta:

Zuwa ga Mansurah Isa, zan baki shawara, ki bar maganar nan ta wuce domin na gaba da ke sun kira ni don bani haƙuri kan kuskuren da akayi da gangan. Ba ki buƙatar sai kin zama mai aron bakin wasu kina ci musu albasa. Ciao.

Ƙanzon kurege ne” Rahama Sadau ta musanta kasancewa cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu

A wani labarin na daban kuma, Rahama Sadau ta nesanta kanta da kwamitin yaƙin neman Tinubu.

Jarumar finafinan Kannywood da Nollywood Rahama Sadau ta nesanta kanta da kasancewa cikin kwamitin mata na yaƙin neman zaɓen Tinubu/Shettima a zaɓen shekarar 2023.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe