Wani abin jimami ya auku a jihar Kwara inda wani matashi ya halaka ƙanin sa yayin gwada maganin bindiga.
Matashin mai suna Abubakar Abubakar ya harbi ƙanin sa har lahira mai suna Yusuf Abubakar ɗan shekara 12, domin gwada ingancin sabon maganin bindigan da suka siyo. Jaridar Daily Trust ta rahoto.
Mahaifin yaran yana da bindigar farauta
Abubakar mamacin ƴaƴan wani mafarauci ne a ƙaramar hukumar Kaiama ta jihar Kwara.
An samo cewa lamarin ya auku ne a ranar Lahadi, sannan matashin Abubakar yayi ɓatan dabo tun bayan aukuwar lamarin. Ya gudu ne bayan ya aikata wannan ɗanyen aikin.
Hukumomi sun tabbatar da aukuwar lamarin
Da yake magana kan lamarin a ranar Litinin, kakakin hukumar ƴan sandan jihar Kwara, Okasanmi Ajayi, yace kwamishinan ƴan sandan jihar Paul Odama, ya bayar da umurnin a gudanar da bincike.
Bayan sun sha maganin bindigan, babban yaron ya ɗauko bindigar farauta ta mahaifin sa sannan ya harbi ƙanin sa, maganin bai yi aiki ba wanda nan take Yusuf ya rasu a wurin.
Okasanmi ya shawarci iyaye da su riƙa sa ido kan abubuwan da yaran su ke aikatawa.
Yakamata su dai na yin abubuwan da ba su dace ba domin hana aukuwar irin wannan lamarin a nan gaba.
A cewar kakakin ƴan sandan
Yaron da ya hangame baki yayin faretin cikar Najeriya 62 da samun ‘yanci na shan caccaka
A wani labarin na daban kuma, yaron da ya hangame baki yayin faretin bikin cikar Najeriya shekara 62 da samun ƴancin kai na shan caccaka.
Yayin da Najeriya tasha shagalin cikarta shekaru 62 da samun ‘yancin kai, abubuwa da na daukar hankali duk sun wakana amma akwai hotunan da su ka fi daukar hankula.
A cikin hotunan da BBC Hausa ta wallafa na shagalin da aka yi a Eagle Square, wanda sojoji su ka yi fareti mai daukar hankula, hoton wani yaro duk ya fi tafiya da imanin mutane.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com