Yayin da Najeriya tasha shagalin cikarta shekaru 62 da samun ‘yancin kai, abubuwa da na daukar hankali duk sun wakana amma akwai hotunan da su ka fi daukar hankula.
A cikin hotunan da BBC Hausa ta wallafa na shagalin da aka yi a Eagle Square, wanda sojoji su ka yi fareti mai daukar hankula, hoton wani yaro duk ya fi tafiya da imanin mutane.
A hoton, an ga yadda yaron ya tsaya a sahun gaba yana bai wa sauran yara irinsa umarni yayin da ya zake tare da hangame bakinsa iyakar dagewarsa.
Nan da nan mutane su ka nufi Kasan hoton inda su ka dinga caccakarsa, har wasu ke ganin zakewarsa ta yi yawa har da zai kusa yaga bakinsa akan Najeriya.
Wasu kuma su na kallon kamar tsabar kishin kasa ne da yake yi tasa har ya bayar da karfinsa wurin yin hakan.
LabarunHausa ta garzaya karkashin hoton inda ta tsinto wasu daga cikin tsokacin jama’a:
Moh’d Ghazali H. Danja yace:
“Kaje ka yaga bakinka akan qasar nan aqi biyan iyayenka diyya wllh.”
Alamin Junaid Ibrahim yace:
“Allah sarki Yaro yarone. Bazamu fadamaka ba sai kagani da idonka tukunna. Ba najeria bace, ta isa kowa Riga da wando.”
Usman Alhassan Abubakar yace:
“Wallahi yunwace tasa yake bude baki haka.”
Comr Salisu Ado Zaitawa yace:
“Amma dai wannan jikan Aisha buhari ne ko.”
Abass Jibo yace:
“A samu man kade a shafa me a bakin sa in zai yi bacci zai samu sauki.”
Ashir Ahmed El-Rufai yace:
“Bawan Allah, Allah yasa kada ayi disappointing dinka wata rana.”
Nasir Mustapha Liman yace:
“Kaga ja’iri kamar tsuntsu yanajin yunwa !!! Za kazo kana istigfari ne.”
Hannatu Amos Waga tace:
“Allah sarki ji yanda yana wage baki ma Nigeria.”
Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta nemi afuwar ‘yan Najeriya kan matsalar tattalin arziki da ake fama da shi tun shekarar 2015
Uwargidan shugaban kasar Najeriya, Aisha Buhari a ranar Juma’a, 30 ga watan Satumba, ta nemi afuwar ‘yan Najeriya game da matsalar tattalin arziki da ake fuskanta a fadin kasar tun bayan hawan mijinta kan karagar mulki.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, Aisha ta nemi afuwar ne a lokacin da take jawabi a wajen taron sallar Juma’a na musamman da kuma lacca na musamman na ranar samun ‘yancin kai karo na 62 mai taken ‘Shura: The Islamic Foundation of True Democracy’ a dakin taro na masallacin kasa dake Abuja.
Ta yi nuni da cewa duk da cewa gwamnati mai ci ta gaza amma akwai bukatar kowa da kowa ciki har da malaman gargajiya da na addini su hada kai don samar da ingantacciyar Najeriya. Dole ne dukkan ‘yan Najeriya su hada kai domin kawo karshen wahalhalun da ake ciki.Uwargidan shugaban kasar ta kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi addu’ar samun nasarar zabe mai zuwa da kuma shirin mika mulki a yayin da gwamnatin Buhari ke shirin ficewa daga ofis.
“Mai yiwuwa gwamnatin ta gaza, amma ina so in yi amfani da wannan dama domin neman gafara daga Malamai da ‘yan Najeriya baki daya. Ya kamata dukkanmu mu hada kai domin samun ingantacciyar Najeriya. “Masu girma manyan baki, mun fahimci cewa tantance Nairar mu,da kuma farashin canji ya shafi tattalin arzikinmu wanda hakan ya jawo wahalhalu ta fuskar ilimi da lafiya da sauran ayyukan yau da kullum na ‘yan kasa. .”
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com