34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Yadda nayi lalata da sama da maza 500 don tsallakawa Turai -Budurwa

LabaraiYadda nayi lalata da sama da maza 500 don tsallakawa Turai -Budurwa

Wata matashiyar budurwa ƴar Najeriya ta bayyana wahalhalun da ta sha a kan hanyar  tafiya cirani zuwa nahiyar Turai.

Matashiyar budurwar ta fito ne daga jihar Delta a yankin Kudu maso Kudu na Najeriya, sannan ta na sana’ar gyaran gashi.

A wata tattaunawa da BBC Hausa tayi da budurwar ta bayyana cewa wani mai safarar mutane ne ya yaudareta cewa yana da ƴar’uwa mai gyaran gashi a Turai, sannan Turawa na son yadda ƴan Najeriya ke gyaran gashi.

Ta dai faɗa a hannun masu safarar mutane tana da shekara 20 a shekarar 2016.

Yadda tafiyar su ta fara.

Ta fiyarmu ta Nijar ta fara daga Nijar ne, mun bi ruwa mun bi rana, mun shiga sahara kuma mun kusa kwashe wata guda cikinta.

Wani buzu ne ya kwashe mu a motarsa, muka ɗauki hanya banda akwai sauran kwana da tuntuni na mutu a wannan saharar, motar da muka shiga muna da yawa mun kai 20 maza da mata a kwance a cikin but ɗin motar.

A kwance muke kafada da kafada, wasu mutane da ke cikin saharan sun tsayar da mu, suka tambayi direban su waye cikin a cikin motar, direban ya ce tinkiyoyi ne a ciki, a raina nace ohh wani nice tinkiya.

Daga ƙarshe sun samu nasarar tsallakawa ƙasar Aljeriya a wani gari da ake kira Oran. A Aljeriya akwai inda  ake jibge ƴan cirani domin fakar idon jami’ai masu kula da shige da fice sai a tsallaka da su ƙasar Morocco.

Sun fuskanci cin zarafi a Aljeriya

Budurwar ta bayyana cewa sun fuskanci con zarafi sosai a sansanin da aka ajiye su a ƙasar Aljeriya, inda maza ke shigowa suna amfani da su. Wasu daga cikin mazan dake amfani da su na ɗauke da cutar ƙanjamau.

A kan idon su wasu daga cikin mazan suka mutu masu ɗauke da cutar ta ƙanjamau.

Budurwar ta fara karuwanci

Bayan isar su Morocco ta nemi da ta gudu amma saidai an gaya mata cewa sai dai ta fanshi kanta wanda hakan ya sanya ta fara karuwanci don tara kuɗaden.

Da aka kai ni Morocco sai na nemi na kama gabana a Casablanca, sai aka ce ai bani da ƴancin tafiya saboda ana bi na bashi, matar da ta biya kudi aka yi jigila da ni daga Najeriya zuwa.”

Dirham D30,000 kwatankwacin yuro €4,000 ake nema daga hannuna, sune kudin jigilar, ba ni da yadda zan yi na sami waɗannan kuɗin, don haka ba ni da wani zabi sai dai na yi karuwanci.

Sai da budurwar ta yi zaman gidan na kusan aƙalla shekara biyu da rabi kafin ta iya biyan kudin da ake binta.

Ta bayyana cewa idan za a kwana D300 ake biyanta, sannan idan kuma kwanciyar ta dan lokaci ce D200 ake biya, kuma ko ƙuɗin kwana mutum ya biya, sau biyu kawai zai kwanta da ita a cikin daren.

Sai dai a halin da ake ciki yanzu budurwar ba ta samu ta kai inda take son zuwa ba, sannan kuma a inda take maƙale yanzu ba ta samun wani abin a zo a gani wanda za ta nuna a matsayin riba idan ta koma gida.

“Ina jin ƙamshin mutuwa wata bakwai kawai suka rage min” Cewar budurwa cikin kuka

Bidiyon wata budurwa wacce tayi iƙirarin cewa wata bakwai kawai ya rage mata a duniya ya sosa zuƙatan mutane a yanar gizo.

Budurwar mai suna Malkai ta garzaya manhajar TikTok cikin kuka inda ta koka kan yadda ta gaji sannan ta rasa ƙwarin guiwar cigaba da rayuwa.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe