31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Gajiyar tafiya ce, Martanin Fati Bararoji akan hotonta wanda aka ganta a komade

LabaraiKannywoodGajiyar tafiya ce, Martanin Fati Bararoji akan hotonta wanda aka ganta a komade

A safiyar jiya ne aka dinga yada wasu hotunan tsohuwar jarumar Kannywood, Fati Bararoji wacce tayi tashe a kwanakin baya a soshiyal midiya inda aka ganta duk ta komade, Fim Magazine ta ruwaito.

A yadda aka santa da cikarta da surarta, a hotunan duk an ga yadda ta zaizaye ta tsiyaye sannan tsufa ya fara bayyana karara a fuskarta, inda wasu su ka dinga zargin ciwo ne ya tasa ta gaba.

Sai dai Mujallar Fim ta nemi sanin karin bayani har wurin ita jarumar, inda aka zargi ta yi ciwon, ashe ba haka abin yake ba. An gano cewa jarumar ta wallafa hoton ne a status din TikTok dinta, wanda tun daga nan mutane da dama su ka dinga yadawa har da masu mata fatan samun lafiya akan cutar da ke damunta.

Yayin da Mujallar fim ta kirata a waya, ta bayyana cewa:

Na yi mamakin yadda naji mutane na ta surutai kala-kala akan hotunana. Har da masu cewa ba ni da lafiya. To ni lafiya ta kalau kuma ban yi fama da wani ciwo ba.

Na dai san na yi tafiya zuwa Abuja, daga can na wuce Sokoto don halartar wani biki, daga nan na dawo Kano.

Yanayin tafiyar da kuma gajiya ne duk su ka sanya na fada, kuma sai na dauki hotunan da aka dinga zargin ba ni da lafiya. Gaskiya lafiyata kalau. Gajiyar tafiya ce kawai.

Daga neman magani: Mai maganin gargajiya ta mallake matar aure, ta tatse kudadenta tare da bautar da ita

Ana zargin wata mai maganin gargajiya, Hauwa da rikidewa ta koma amfani da sihiri wurin tatse wata matar aure wacce ta je neman magani a wurinta kasancewar mijinta ba ya da lafiya, Dala FM ta ruwaito.

Kamar yadda matar ta shaida, har sadakin auren diyarta sai da ta amshe sannan ta sanya ta ta sayar da gonarta ta mika mata kudaden.

Ta ci gaba da bayyana cewa har tura yaranta gidan matar take yi su na yi mata wanki mai yawan gaske da aikace-aikace.

Ita Hauwa ta cuce ni. Da zimmar cewa zata taimake ni mai gidana ba lafiya. Tun daga lokacin da naje neman magani ta mallake ni ni da yarana. Duk abinda tace mu yi shi muke yi babu makawa.

Idan ta ce ma kar ka kula mahaifiyar da ta haifeka ma baza ka kulata ba. Atamfofi, ta ce Mai Dawa ya ce a kawo atamfofi. Omo ta ce azo ayi mata wanki. Wallahi sai yarana su yi mata wanki sai su yi mata wanki mai yawa kamar omo ukun nan da ake siyarwa N110. Girki, aike, ta dai mayar damu kamar bayinta.

Lokaci guda Ubangiji Allah ya bani damar in yi magana akan cutar da ta yi min. Shi kanshi filin da ta sanya na siyar kudin ita na mika mawa. Ba za ta cuce ni ba, duk lokacin da na nema ba za ta hana ni ba. Idan nayi magana ta ce an tafi da kudin Abuja, anje da shi Saudiyya.”

Ta bayyana yadda take hada ta da iska wadanda za su razana ta da sunan zasu kassara ta da yaranta.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe