Ƴan bindiga sun sace wani basarake tare da matar sa da kuma direban sa a jihat Kwara.
Ƴan bindigan sun sace basaraken na Owa Anire, Abdulrahaman Lawal Ifabiyi, akan hanyar sa ta komawa gida.
An dai sace basaraken ne da sauran mutum biyun a ƙaramar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa an yiwa basaraken kwantan ɓauna ne a wajen Oba-Isin da Owa Onire a tsakanin Isin da ƙaramar hukumar Ifelodun ta jihar ranar Asabar a yayin da suke dawowa daga wurin wani biki.
Hukumomi sun tabbatar da aukuwar lamarin
Kakakin hukumar ƴan sandan jihar Kwara, Okasanmi Ajayi, ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Lahadi.
A cewar kakakin hukumar ƴan sandan, kwamishinan ƴan sandan jihar Paul Odama, ya tura ƙwararrun jami’ai da ƴan sakai da gaggawa zuwa inda lamarin ya auku.
Ya bayyana cewa an ceto matar basaraken, inda ya ƙara da cewa an cafke wasu mutum biyu da ake zargin suna da hannu a sace basaraken.
Hukumar ƴan sanda na bakin ƙoƙarin ta don ceto basaraken
Yace ana iyakar bakin ƙokari domin ganin an ceto basaraken da kuma direban sa.
Kwamishinan ƴan sandan ya ƙara jaddada cewa ba daga ƙafa ga kowane irin laifuka da masu aikata su sannan ya kuma shawarci ɓata gari da su tattara ƴan komatsan su, su yi ƙaura daga jihar Kwara, domin an kawo jajirtaccen shugaba yanzu.
Inji shi
Kano: Masu garkuwa da mutane sun sako basaraken da su ka ɗauke, sun yi ram da mai kai kuɗin fansa
A wani labarin na daban kuma, masu garkuwa sun sako wani ɓasaraken da suka yi garkuwa da shi a Kano, sun yi ram da wanda ya kai kuɗin fansa.
Abdulyahyah Ilo, magajin garin Karfi cikin ƙaramar hukumar Takai, a jihar Kano, ya samu ‘yanci daga hannun masu garkuwa da mutane.
Sai dai masu garkuwa da mutanen, sun riƙe wani farfesa a jami’ar kimiyya da fasaha ta jihar Kano (KSTU), Wudil, Huzaifa Karfi, wanda yaje kai kuɗin fansar.
Masu garkuwa da mutanen sun halaka mutane shida, waɗanda su kayi ƙoƙarin ceto basaraken lokacin da su kaje ɗaukar sa.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com