34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Hisbah a Zamfara ta fashe giya da ta kai ta Naira miliyan 50

LabaraiHisbah a Zamfara ta fashe giya da ta kai ta Naira miliyan 50

Hisbah a Zamfara ta rufe katafaren otal

Hukumar hisbah a Zamfara ta bayyana cewa sunyi nasarar kame tare da fashe kwalebanin giya da suka kai na kimanin kuɗi har Naira miliyan 50 a jihar.

Hakanan hukumar ta sanar da rufe wani shahararren otal mai suna ‘Top town hotel’ wanda yake a Igala kwatas dake cikin Gusau babban birnin jihar ta Zamfara, kamar yadda muka samu daga jaridar Tribune.

Da yake jawabi a ranar Lahadi yayin gabatar da jawabi tare da bayyana waɗanda aka kama dangane da hakan tare da nuna nau’o’in giya daban-daban da aka kama, Kwamishinan dake kula da zangon wato Usman Buhari Maijega, ya bayyana cewa sun kulle wani shahararren katafaren otal mai suna ‘Top Town Hotel’ dake nan cikin Gusau.

Ya bayyana cewa dalilin da yasa suka rufe otal ɗin shine saboda yawan ƙorafe-ƙorafen da suke samu daga mutanen dake maƙwabtaka da otal ɗin kan cewar masu gudanar da sha’anin otal ɗin na takura musu.

Hisbah ta cafke manajan otal ɗin

Ya ƙara da cewa a yayin da suka kai samame otal ɗin sun samu nasarar cafke manajan otal ɗin, maza uku da kuma mata uku. Sannan yace sunyi nasarar kama katan 10 na giya duk a otal ɗin.

“Mun kama manajan otal ɗin kuma zamu gurfanar dashi a gaban kotu domin ya fuskanci hukunci irin na shari’ar Musulunci saboda yana taimaka ma da kuma ƙarfafa aikata zinace-zinace.”

Hisbah A Zamfara bakowa ƙafa ba

Ya tsayu akan cewa a irin wannan batu, babu wani wanda za’a ɗaya ma ƙafa sabili da kamar yadda ya bayyana cewa: “hukumar hisbah ta ɗauki alƙawarin hukunta duk wani aiki da aka aikata wanda ya saɓa da dokokin addinin Muslunci.”

Kwamishinan ya tabbatar da cewa tuni jami’an su suka ragargaje giyar wacce takai ta aƙalla Naira miliyan 50, kuma nan bada jimawa ba ma zasu ƙara ƙone wani kaso na daga tarin giyar da suka kama a baya.

A wani labarin kuma kunji cewa an samu gawarwakin mata guda 2 a ofishin shugaban Asibiti. An samu gawarwakin wasu mata guda biyu da acan baya aka shelanta ɓacewar su a ofishin wani babban likita kuma daraktan babban asibitin garin Kaiama dake jihar Kwara.

Daga cikin gawarwakin da aka gano a ofishin likitan da akwai gawar wata mata da aka bayyana sunanta da Nafisah Halidu wacce aka sanar da ɓacewar ta tun watan Nuwamban shekarar 2021.

Jami’in hulɗa da jama’a na ƴan sandan jihar ta Kwara Okasanmi Ajayi, ya tabbatar ma da manema labarai hakan a ranar Lahadi inda kuma ya bayyana cewa yanzu haka wanda ake tuhuma mai suna Dr Adio Adebowale, na hannun ƴan sandan jihar Edo a tsare bisa wani laifin kisan na daban da ya aikata a can.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe