An samu gawarwakin ne a ofishin babban likitan asibitin
An samu gawarwakin wasu mata guda biyu da acan baya aka shelanta ɓacewar su a ofishin wani babban likita kuma daraktan babban asibitin garin Kaiama dake jihar Kwara.
Daga cikin gawarwakin da aka gano a ofishin likitan da akwai gawar wata mata da aka bayyana sunanta da Nafisah Halidu wacce aka sanar da ɓacewar ta tun watan Nuwamban shekarar 2021.
Jami’in hulɗa da jama’a na ƴan sandan jihar ta Kwara Okasanmi Ajayi, ya tabbatar ma da manema labarai hakan a ranar Lahadi inda kuma ya bayyana cewa yanzu haka wanda ake tuhuma mai suna Dr Adio Adebowale, na hannun ƴan sandan jihar Edo a tsare bisa wani laifin kisan na daban da ya aikata a can kamar yadda jaridar Leadership ta wallafa.

“Domin cigaba da faɗaɗa bincike, Kwamishinan ƴan sandan jihar kwara Mr Paul Odama ya tuntuɓi rundunar ƴan sandan jihar ta Edo don ganin an dawo da wanda ake tuhuma zuwa Kwara don amsa tambayoyi akan gawarwakin da aka gano a ofishin shi.” inji Ajayi.
An ƙwaƙulo ɗaya daga cikin gawarwakin a ƙasan daɓen ofishin
Kakakin ƴan sandan ya bayyana cewa ɗaya daga cikin gawarwakin an ƙwaƙulo ta ne a ƙasan simintin ofishin, a yayin da ɗayar kuma aka ƙwalulo ta a wani ɓangaren ofishin cikin gurin da ake zubar da shara da kuma tarkace.
Kakakin ƴan sandan ya ƙara da cewa: “Rundunar ƴan sandan jihar Kwara na son sanar ma da ɗaukacin al’ummar jihar sakamakon binciken da Kwamishina ƴan sandan jihar Kwara Paul Odama ya bada umarnin a gudanar.”
“A yayin da yake duba wasu ƙorafe-ƙorafe da mutane suka shigar bayan fara aiki a matsayin Kwamishinan ƴan sandan jihar Kwara, Kwamishinan ya ci karo da wani ƙorafi da aka shigar kan ɓatan wata mata Nafisat Halidu ‘Mace’ a Kaiama, ƙaramar hukumar Kaiama jihar Kwara a ranar 21/11/2021. Kwamishinan ya bada umarnin kafa kwamitin bincike cikin gaggawa wanda muƙaddashin ƴan sanda daga ofishin binciken manyan laifuka na jihar don binciko abubuwan da suka wakana.
“Bisa umarnin Kwamishina, an fara binciken a 30/09/2022. Jami’an bisa bin bayanan wanda ake tuhuma wato Dakta Adio Adeyemi Adebowale dake hannun ƴan sandan Edo wanda ya amsa cewa ya kashe budurwar shi wata mai suna Ifeoluwa wacce ta ɓace a yankin Tanke dake Ilorin a wani lokaci a shekarar 2021, wacce daga bisani aka samu gawarta a cikin daji a yankin Alapa na Ilorin a inda ya jefar da ita.
A guri daban-daban aka samu gawarwakin
“Abun mamaki, likitan da ake tuhuma shine shugaban babban asibitin garin Kaiama. Masu binciken sun je ofishin likitan a babban asibitin Kaiama, inda suka ɓalle ofishin shi sannan suka fasa wani sabon daɓen siminti da aka yi inda anan ne suka ci karo da gawar wata mata da ba’a iya ganewa ba a lokacin.
“A cigaba da bincike a cikin ofishin, jami’an sunyi nasar gano wata gawar wata matar a cikin gurin zuba shara wacce aka bayyana sunan ta da Nafisat Halidu data ɓata a baya, wacce mijinta da sauran mutanen yankin dake a gurin suka iya tantancewa.
“Daga cikin ƙarin abubuwan da aka gano akwai wayoyin hannu guda biyu da aka samu a cikin jakar ɗaya daga cikin matan. Sannan an samu jakunkunan mata guda 2, hular gashi, mayafi, da kuma ɗan kanfai na mata.”
A wani labarin kuma, manoman Kano sun koka kan ɓarnar ambaliyar ruwa. Ambaliyar ruwan dai wacce ke janyo wa manoman asarar kayan amfanin gona tana faruwa ne sakamakon ɓallewar da ruwa yake yi daga dam ɗin Tiga.
Wannan na zuwa ne dai watanni kaɗan da aka hana manoman yin amfani da gonakin nasu wajen noma rani sakamakon ƴan gyare-gyare da akayi a wancan lokacin. Sai dai kuma duk da haka gashi yanzu dam ɗin na zame musu masifa sanadiyyar kwararowar ruwan dake cinye musu gonaki.
“Bamu samu damar noma gonakin mu ba a lokacin rani sakamakon rufe dam ɗin da aka yi saboda wasu ƴan gyare-gyare, alhalin kuma kusan duk mun dogara ne ga dam ɗin lokacin noman rani. Muna tsammanin mu samu mu ɗan farfaɗo a lokacin noman damina sai dai kuma gashi yanzu dam ɗin yana cinye mana gonaki.” inji ɗaya daga cikin manoman.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com