31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Yadda wani mutumi ya gina gida mai daki 3 da gororin roba guda 14,800

LabaraiYadda wani mutumi ya gina gida mai daki 3 da gororin roba guda 14,800
b291af959f87a628

Injiniya Yahaya Ahmed Injiniyan da ya gina gida a Kaduna inda ya yi amfani da gororin roba guda 14,800 a matsayin bulo. Premium Times ta rahoto cewa Ahmed shine daraktan wata kungiya mai zaman kanta, Developmental Association of Renewable Energies in Nigeria (DARE). Legit.ng ta tattaro cewa injiniyan ya ce kungiyarsa ta gina gidan ne domin karfafa sarrafa kayan da basuda amfani tare da samar da ayyukan yi a Najeriya.
Da yake bayyana tsarin ginin gidan, Ahmed ya ce ma’aikatan sun cika kwalaben robobin da yashi tare da daidaita su ta hanyar hada su da igiyoyi. Ya ce ginin shi ne irinsa na farko a yankin kudu, inda ya ce ya fi arha gina shi saboda ana samun kayayyakin gini a kan tituna da wuraren zubar da shara. Gidan yana da dakuna uku, bandaki da kicin. Ta fuskar karfi da karko Ahmed ya ce gidan ya fi gidajen bulo karko kuma zai iya dauwama sama da shekaru 300 idan an gina shi yadda ya kamata kuma a tsanake.” A cewarsa,wuta ba zai iya cinye shi ba, harsashi ba zai iya huda shi ba, kuma yana iya jure girgizar kasa. ya dace da kowane irin sauye-sauyen yanayi, Ahmed ya ce duk wanda ke da fasahar gini za a iya amfani da shi a matsayin aiki wajen gina gida, ya kara da cewa kungiyarsa ta horar da matasa da dama.

Ahmed ya ce sun fara wannan aikin ne don rage yawan robobin da ke gurbata muhalli da haddasa cututtuka. A martanin da ya mayar dangane da shirin ginin, mataimakin daraktan masu ba da rahotanni kan yanayin Afirka, Piman Hoffman, ya bukaci gwamnatin Najeriya da ta tallafa wa kamfanonin da ke sabunta kayyaki domin ceto al’ummar kasar daga barazanar gurbatar yanayi. Ya yi nuni da cewa, robobi babbar barazana ce ga wanzuwar mutane, dabbobi da dukkan halittu masu rai.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe