31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

“Ƙanzon kurege ne” Rahama Sadau ta musanta kasancewa cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu

Labarai"Ƙanzon kurege ne" Rahama Sadau ta musanta kasancewa cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu

Jarumar finafinan Kannywood da Nollywood Rahama Sadau ta nesanta kanta da kasancewa cikin kwamitin mata na yaƙin neman zaɓen Tinubu/Shettima a zaɓen shekarar 2023.

A ranar Asabar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ta bayyana sunayen mata ƴan kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar.

Jerin sunayen ya ƙunshi wani ɓangare na masu nishaɗantarwa, wanda ke a ƙarƙashin jagorancin jarumar finafinan Nollywood Joke Silva. Jaridar The Cable ta rahoto.

An saka sunan Rahama Sadau a cikin kwamitin tare da sauran manyan jaruman Nollywood irin su Mercy Johnson, Toyin Adegbola, Esther Wright, Rose Odika, Hadiza Kabara, Fathia Balogun, da Sola Kosoko.

Rahama Sadau ta ƙaryata cewa tana cikin kwamitin

Da take magana a shafin Twitter akan bayyanar sunan ta a cikin kwamitin, Rahama Sadau ta ƙaryata kasancewa a cikin jirgin yaƙin neman zaɓen Tinubu/Shettima.

Rahama Sadau tace ba a nemi shawarar ta ba kafin saka sunan ta a cikin jerin ƴan kwamitin.

Jarumar ta kuma yi mamakin yadda akayi har sunan ta ya shiga cikin ƴan kwamitin ba tare da iznin ta ba.

Wannan tsantsagoron ƙarya ce… Bani da masaniya akan wannan… Ban san ta yadda akayi suna na ya shigo cikin wannan jerin ba, bani da wata alaƙa kowace iri da wannan.

APC ba tayi martani akan maganar da jarumar tayi

Har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, jam’iyyar APC ba tace komai ba dangane da maganar da Rahama Sadau tayi.

Tinubu yana ɗaya daga cikin na sahun gaba a cikin ƴan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, tare da Atiku Abubakar na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Peter Obi na jam’iyyar Labour Party (LP)

Anya kina tuna mutuwa kuwa?: Sabbin hotunan Rahama Sadau sun tada kura a Twitter

Shahararriyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta sha caccaka a shafinta na Twitter bayan ta saki wasu hotuna da su ka bayyana jikinta.

Hotunan sun tayar da kura inda masu zaginta su ka dinga zaginta yayin da wasu su ke mata fatan shiriya.

Ba sabon abu bane ganin jarumar da irin wannan shigar kasancewar ta dade tana janyowa kanta zagi don kusan duk shekara sai an yi caa akanta

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com


Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe