34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta nemi afuwar ‘yan Najeriya kan matsalar tattalin arziki da ake fama da shi tun shekarar 2015

LabaraiUwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta nemi afuwar ‘yan Najeriya kan matsalar tattalin arziki da ake fama da shi tun shekarar 2015
e3d7f26475339369

Uwargidan shugaban kasar Najeriya, Aisha Buhari a ranar Juma’a, 30 ga watan Satumba, ta nemi afuwar ‘yan Najeriya game da matsalar tattalin arziki da ake fuskanta a fadin kasar tun bayan hawan mijinta kan karagar mulki.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, Aisha ta nemi afuwar ne a lokacin da take jawabi a wajen taron sallar Juma’a na musamman da kuma lacca na musamman na ranar samun ‘yancin kai karo na 62 mai taken ‘Shura: The Islamic Foundation of True Democracy’ a dakin taro na masallacin kasa dake Abuja.
Ta yi nuni da cewa duk da cewa gwamnati mai ci ta gaza amma akwai bukatar kowa da kowa ciki har da malaman gargajiya da na addini su hada kai don samar da ingantacciyar Najeriya. Dole ne dukkan ‘yan Najeriya su hada kai domin kawo karshen wahalhalun da ake ciki.Uwargidan shugaban kasar ta kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi addu’ar samun nasarar zabe mai zuwa da kuma shirin mika mulki a yayin da gwamnatin Buhari ke shirin ficewa daga ofis.
Mai yiwuwa gwamnatin ta gaza, amma ina so in yi amfani da wannan dama domin neman gafara daga Malamai da ‘yan Najeriya baki daya. Ya kamata dukkanmu mu hada kai domin samun ingantacciyar Najeriya. “Masu girma manyan baki, mun fahimci cewa tantance Nairar mu,da kuma farashin canji ya shafi tattalin arzikinmu wanda hakan ya jawo wahalhalu ta fuskar ilimi da lafiya da sauran ayyukan yau da kullum na ‘yan kasa. .”

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe