31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Manoman Kano sun koka kan ɓarnar ambaliyar ruwa

LabaraiManoman Kano sun koka kan ɓarnar ambaliyar ruwa

Manoma sunyi asarar amfanin gona da dama

Manoma a Kano sun koka kan yadda ambaliyar ruwa ke cigaba da mamaye musu gonakin wanda hakan ke janyo asarar amfanin gona na miliyoyin kuɗade.

Ambaliyar ruwan dai wacce ke janyo manoman asarar kayan amfanin gona tana faruwa ne sakamakon ɓallewar da ruwa yake yi daga dam ɗin Tiga.

Wannan na zuwa ne dai watanni kaɗan da aka hana manoman yin amfani da gonakin nasu wajen noma rani sakamakon ƴan gyare-gyare da akayi a wancan lokacin. Sai dai kuma duk da haka gashi yanzu dam ɗin na zame musu masifa sanadiyyar kwararowar ruwan dake cinye musu gonaki.

“Bamu samu damar noma gonakin mu ba a lokacin rani sakamakon rufe dam ɗin da aka yi saboda wasu ƴan gyare-gyare, alhalin kuma kusan duk mun dogara ne ga dam ɗin lokacin noman rani. Muna tsammanin mu samu mu ɗan farfaɗo a lokacin noman damina sai dai kuma gashi yanzu dam ɗin yana cinye mana gonaki.” inji ɗaya daga cikin manoman.

Manoman Kano sun koka
Ambaliyar ruwa/ Dailytrust

Manoma da dama sun dogara ga dam ɗin Tiga

Shekaru da dama, dam ɗin Tiga ya kasance wata babbar kafa da yankuna da dama ke amfani dashi wajen yin banruwa a jihar Kano. Dam ɗin ya zama kamar wata rijiyar mai ne ga manoma dake noman rani a Kano, haka nan ma kuma ga makiyaya dake shayar da dabbobin su a lokacin rani.

An gina dam ɗin Tiga dai ne a shekarar 1974 a lokacin mulkin Audu Baƙo, wanda ya kasance gwamnan Kano na wancan lokacin. An gina dam ɗin ne domin tabbatar da samuwar isasshen abinci da kuma tabbatar da amfani da faɗin ƙasar noman dake jihar Kano.

Faɗi da tsayin dam ɗin na Tiga yakai aƙalla kilomita 178 sannan kuma yana da girman ɗaukar ruwa har na kusan santimita miliyan biyu. Dam ɗin dai ya kasance kafa ce dake bada damar gudanar da wani shirin na musamman kan noman rani a Kano. Haka nan ya kasance wajen gudanar da wasu muhimman ƙudurori da dama na noman rani a Kano.

Sai dai kuma wani faifan bidiyo da yayi ta yawo a kafafen sada zumunta a satin ɗaya gabata ya sanya firgici a zukatan manoma dama dai sauran al’umma. Bidiyon ya nuna irin yadda dam ɗin na Tiga ya ɓalle da kuma irin ɓannar da yayi wajen lalata gadoji, manyan tituna, da kuma gonaki.

Gwamnati ta musanta iƙirarin manoman

Sai dai kuma a nata ɓangaren, gwamnatin tarayya ta musanta labarin a yayin wata ziyarar duba aiki da jami’ai suka kai, inda suka ce dam ɗin yana nan yadda ya kamata kuma matakin ruwan ya dam ɗin bai ɗaga ba.

Sai dai kuma manoma da mazauna yankin na Tiga dama sauran maƙwabta ƙananan hukumomi sun jaddada cewa lallai fa dam ɗin ya ɓalle kuma yayi musu ɓarna. A dalilin hakan ne suke riƙon gwamnati data zo ta kawo musu agaji.

Wani bincike da jaridar Dailytrust tayi a Bebeji, da kuma wani ɓangare na ƙananan hukumomin Kura, Rano da kuma Kumbotso ya tabbatar da yadda ruwan ya kwarara zuwa gonaki inda yanzu haka manoma da dama suka kasa yin aiki a gonakin nasu.

Aminu Shehu, wani manoma a Bebeji ya bayyana cewa ya rasa komai na daga amfanin gonar shi sakamakon ambaliyar. Ruwa ya shanye duka masarar da ya noma a wannan shekarar.

“Ruwan bara da akayi ya zo mana da matsaloli sakamakon fara shi da akayi da wuri wanda hakan ya janyo mana asarar. Ruwan bana kuwa ya zo mana a daidai kafin zuwan wannan ɓallewar ruwan daga dam wanda ya shanye mana gonaki. A yanzu haka da muke magana da kai, bazan iya zuwa gonata ba sai dai akan kwale-kwale, na rasa komai dake gonar tawa.” inji manomin.

Wani manomin malam Sagiru Gulu ya bayyana cewa ruwa ya cinye fiye da rabin dawar shi dake gona inda a yanzu haka bazai iya zuwa gonar tashi ba saboda ruwan da ya mamaye ko ina.

“Kaga wata bishiya can? Daga nan ne gona ta ta fara amma a yadda kake iya gani yanzu duk ruwa ya mamaye ta kuma har yanzu ruwa na ta ƙara kwarara ciki, ban sani ba ko sauran ɓangaren zai tsallake. Abinda ya rage mana shine kawai muyi ta addu’o’i tare da zura ma sarautar Allah ido.” inji malam Sagiru.

A wani labarin na daban kuma, Sojoji sun ceto ɗaya daga ƴan matan chibok ɗauke da ƴaƴa huɗu. A ranar Alhamis ne dai jami’an sojin Najeriya suka yi nasarar kuɓutar da ɗaya daga cikin ƴan matan Chibok da mayaƙan boko Haram suka sace a makarantar sakandiren Chibok a 2014.

Wannan matashiya dai wacce aka bayyana sunanta da Yana Pogu ta samu damar kuɓuta ne ta dalilin jami’an sojojin Najeriya ƙarƙashin wata rundunar ta musamman da aka yi ma laƙabi da ‘Operation Haɗin Kai’ kamar yadda the cable ta ruwaito.

Watanni huɗu da suka gabata nan baya, matashiya Yana Pogu ta kasance ta haifi ƴaƴa tagwaye a lokacin tana hannun ƴan ta’addan da suka yi garkuwa da ƴan matan Chibok ɗin.

Sai dai manema labaran da suka samu damar ganawa da ita sun bayyana cewa a yayin da aka kuɓutar da ita, ƴaƴan basa cikin ƙoshin lafiya, kuma suna ɓuƙatar a duba lafiyar su cikin gaggawa.

Doocivir yace duka ɓangaren guda biyu sun aminta da a raba auren. Kuma harma wanda akayi ƙara wato mijin ya buƙaci kotu da ta cika ma matartashi burinta na rabuwar auren.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe