24.1 C
Abuja
Tuesday, January 31, 2023

2023: Dalilin da yasa PDP zata lashe zaɓen shugaban ƙasa -Atiku Abubakar

Labarai2023: Dalilin da yasa PDP zata lashe zaɓen shugaban ƙasa -Atiku Abubakar

Ɗan takarar kujerar shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) a babban zaɓen shekarar 2023, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana cewa jam’iyyar sa zata iya lashe zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.

Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne a jihar Gombe bayan ya ƙaddamar da ofishin yaƙin neman zaɓen sa a jihar. Jaridar Vanguard ta rahoto.

Ya bayyana dalilan sa

Jam’iyyar PDP zata iya lashe zaɓen shugaban ƙasa saboda kasancewar ta ɗaya daga cikin tsofaffin jam’iyyu a ƙasar nan.

Inji shi

Atiku Abubakar ya bayyana cewa jam’iyyar PDP na da magoya baya sosai a jihar Gombe, sannan zata yi amfani da wannan damar domin tabbatar da cewa ta samu nasara a zaɓukan 2023.

Atiku yayi muhimmin kira ga magoya bayan PDP

Ya kuma yi kira ga magoya bayan jam’iyyar PDP a jihar da su kiyayi yin ƙarairayi wurin yaƙin neman zaɓe inda ya buƙace su da su mayar da hankali kan abubuwa masu muhimmanci domin ƙara samun magoya baya.

Ziyarar da Atiku Abubakar ya kai ranar Asabar a jihar Gombe, itace karo na uku da Atiku ya ziyarci jihar a shekarar 2022 a dalilin lamuran da suka shafi siyasa.

Tuni dai aka fara buga kugen siyasa a Najeriya bayan da hukumar zaɓe mai zaman kanta wato INEC, ta bayar da damar a fara yaƙin neman zaɓe a faɗin ƙasar nan.

Ƴan siyasa da dama sun fara azama da zage damtse domin fara neman magoya baya don ganin sun kai ga ci a zaɓukan dake tafe na shekarar 2023.

Atiku Abubakar dai zai yi takara ne da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar PDP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na jam’iyyar NNPP, Peter Obi na jam’iyyar Labour Party da kuma sauran wasu ƴan takara.

An ci zaɓe an gama: Tuni har Atiku ya fara rubuta sunayen ministocin sa -Kakakin yaƙin neman zaɓe

Tuni har ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya fara rubuta sunayen mutane ciki har da na ƴan adawa waɗanda zai yi aiki da su idan ya lashe zaɓe.

Kakakin yaƙin neman zaɓen Atiku, Charles Aniagwu, shine ya bayyana hakan a yayin wata hira da gidan talabijin na Arise kan rikicin cikin gida na PDP

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe