31.1 C
Abuja
Sunday, April 2, 2023

Yadda sojojin Isra’ila suka halaka wani ƙaramin yaro mai shekara 7 ɗan ƙasar Palasɗinu

LabaraiYadda sojojin Isra'ila suka halaka wani ƙaramin yaro mai shekara 7 ɗan ƙasar Palasɗinu

Palasɗinawa mazauna yankin West Bank sun yi jana’izar wani ƙaramin yaro mai shekara bakwai a duniya, Rayan Suleiman.

Mahaifan yaron sun bayyana cewa ya tsoron sojojin Isra’ila ne yayi sanadiyyar rasuwar sa.

A jiya ne dai sojojin Isra’ila suka biyo Rayan Suleiman da shi da ƴan’uwan sa suna tafiya daga gida zuwa makaranta. Jaridar The Islamic Information ta rahoto.

Sun yi iƙirarin cewa sojojin sun buga musu kofa cikin fushi sannan suka yi musu barazanar kamu. Rayan, wanda ɗan ƙaramin cikin yaran uku, ya rasu lokaci kaɗan bayan aukuwar lamarin.

Yadda sojojin suka yi sanadiyyar rasuwar yaron

Mohammed Suleiman, wani ɗan’uwan Rayan, ya shaidawa Al Jazeera cewa bayan Rayan ya dawo gida, sojojin sun biyo shi inda suke ta masa magana cikin fushi.

Sojojin sun yi masa magana cikin fushi cewa shi mai jefa dutse ne. Yayi kaciɓus da wani soja bayan ya ruga, lokacin da Rayan ya ga sojan a gabanshi, ya firgita kawai sai ya faɗi ƙasa cikin tsoro.

Mahaifin Rayan, Yasser Sulaiman, ya bayyana cewa Rayan ya faɗi ƙasa ne bayan yaga sojojin Isra’ilan da suka biyo shi sun bayyana a gaban ƙofar sa.

Ƴayyen Rayan, ƴan shekara takwas da shekara goma, sojojin sun yi musu barazanar kamu. Hatsaniyar da ake yi ce ta sanya Rayan ya sume.

Duk da ƙoƙarin da likitoci suka yi a asibitin Beit Jala, ba a samu an ceto rayuwar sa ba.

Ƴan sandan Isra’ila sun tsare darektan masallacin Al-Aqsa

A wani labarin na daban kuma, ƴan sanda a ƙasar Isra’ila sun tsare darektan masallacin Al-Aqsa.

Ƴan sandan ƙasar Isra’ila sun kama tare da tsare darektan masallacin Al-Aqsa, Sheikh Omar Kiswani.

Jaridar The Islamic Information ta ambato wakilin jaridar WAFA na cewa, ƴan sandan sun cafke malamin sannan suka tsare shi har na zuwa wani lokaci.

Kamar yadda majiyoyi suka bayyana, ƴan sandan sun kwace na’ura mai ƙwaƙwalwa da wasu takardu na Sheikh Kiswani a gidan sa bayan sun yi wa gidan binciken ƙwaƙwaf.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe