34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Sojoji Sun Ceto Ɗaya Daga Ƴan matan Chibok Ɗauke da Ƴaƴa Huɗu

LabaraiSojoji Sun Ceto Ɗaya Daga Ƴan matan Chibok Ɗauke da Ƴaƴa Huɗu

An kuɓutar da ɗaya daga cikin ƴan matan Chibok

A ranar Alhamis ne dai jami’an sojin Najeriya suka yi nasarar kuɓutar da ɗaya daga cikin ƴan matan Chibok da mayaƙan boko Haram suka sace a makarantar sakandiren Chibok a 2014.

Wannan matashiya dai wacce aka bayyana sunanta da Yana Pogu ta samu damar kuɓuta ne ta dalilin jami’an sojojin Najeriya ƙarƙashin wata rundunar ta musamman da aka yi ma laƙabi da ‘Operation Haɗin Kai’ kamar yadda the cable ta ruwaito.

Watanni huɗu da suka gabata nan baya, matashiya Yana Pogu ta kasance ta haifi ƴaƴa tagwaye a lokacin tana hannun ƴan ta’addan da suka yi garkuwa da ƴan matan Chibok ɗin.

Ƴa ƴan suna buƙatar a duba lafiyarsu

Sai dai manema labaran da suka samu damar ganawa da ita sun bayyana cewa a yayin da aka kuɓutar da ita, ƴaƴan basa cikin ƙoshin lafiya, kuma suna ɓuƙatar a duba lafiyar su cikin gaggawa.

Gamayyar jami’an soja da haɗin gwuiwar wani ɓangare na jami’an ƴan sakai na farar hula da ake wa laƙabi da ‘civilian JTF’ ne suka yi nasarar ceto matashiyar a sansanin ƴan ta’addan boko Haram ɗin dake a ƙaramar hukumar Bama dake jihar Borno.

Bayanai da aka samu daga wata majiya ta sirri sun tabbatar da cewa jami’an sunyi musayar wuta tsakaninsu da ƴan boko Haram ɗin. Jami’an daga bisani sun ci ƙarfin ƴan ta’addan inda suka yi nasarar kashe da dama daga cikinsu a yayin da wasu da dama suka tsere da harin harsashi a jikunansu.

Tana cikin ƴan matan Chibok da aka ɗauke a 2014

“A yayin artabun, jami’an sunyi nasarar kuɓutar da Yana Pogu da yaranta guda 4. Pogu dai ta kasance ɗaya daga cikin ƴan matan Chibok wacce itace lamba ta 19 a jerin sunayen yaran da aka ɗauke a wancan lokacin.” inji majiyar tamu.

“An samo ta ne tare da yara ƴan wata huɗu a cikin matsanancin halin rashin lafiya.”

“Wasu daga cikin ƴan ta’addan a yayin da suke ƙoƙarin tserewa sunyi yinƙurin yima jami’an kwanton ɓauna. Sai dai kuma jami’an a sabili da bayanan sirri da suka samu sunyi nasarar fatattakar duka ƴan ta’addan.”

“An samu nasarar kuɓutar da mata da dama bayan artabun, waɗanda duka aka kaisu sansani rundunar sosoji dake garin Bama domin a duba lafiyar su.” majiyar tamu ta ƙara bayani.

Sama da ɗalibai ƴan matan Chibok 200 ne aka sace a shekarar 2014 daga makarantar sakandiren ƴan mata dake garin Chibok a yayin da ƴan boko haram suka kaima garin hari.

Jami’ai sunyi nasarar kuɓutar da dama daga cikin ƴan matan duk da dai har yanzu akwai wasu da dama da har yanzu suke a hannun ƴan ta’addan na boko haram.

A wani labarin na daban kuma, wata kotu dake zamanta a Nyanya dake babban birnin tarayya Abuja ta raba aure na tsawon shekaru goma tsakanin wani miji mai suna Simon da kuma matar shi Blessing Ameh akan dalilin rashin haihuwa.

Jaridar punch ta ranar Asabar ta wallafa a shafin ta cewa alƙali mai shari’a Doocivir Yawe ya raba aure tsakanin miji da matar ne bisa dalilin cewa duka mata da mijin sun gaji da cigaba da kasancewa a tare.

Doocivir yace duka ɓangaren guda biyu sun aminta da a raba auren. Kuma harma wanda akayi ƙara wato mijin ya buƙaci kotu da ta cika ma matartashi burinta na rabuwar auren.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe