32.4 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

Kotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

LabaraiKotu Ta Raba Auren Miji Da Mata A Abuja

Kotu ta raba auren miji da mata saboda rashin haihuwa a Abuja

Wata kotu dake zamanta a Nyanya dake babban birnin tarayya Abuja ta raba aure na tsawon shekaru goma tsakanin wani miji mai suna Simon da kuma matar shi Blessing Ameh akan dalilin rashin haihuwa.

Jaridar punch ta ranar Asabar ta wallafa a shafin ta cewa alƙali mai shari’a Doocivir Yawe ya raba aure tsakanin miji da matar ne bisa dalilin cewa duka mata da mijin sun gaji da cigaba da kasancewa a tare.

Doocivir yace duka ɓangaren guda biyu sun aminta da a raba auren. Kuma harma wanda akayi ƙara wato mijin ya buƙaci kotu da ta cika ma matartashi burinta na rabuwar auren.

“A dalilin hakan, kotu bata da wani zaɓi face ta cika ma mai ƙarar burinta na riƙon a raba auren. Saboda haka, kotu ta rushe auren.” inji alƙalin.

Kotu ta buƙaci a biya dubu 50 gabanin raba auren

“Sannan kotu ta umarci matar data mayar ma mijin nata kuɗin sadakin shi har Naira dubu hamsin (N50,000).”

Ma’aikatar jakadancin labarai ta Najeriya ta ruwaito cewa Ameh ta kai ƙarar Simon kotu ne tana roƙon a raba auren nasu a bisa dalilin cewa auren ya fita daga ranta gaba ɗaya.

Duk matakan da aka ɗauka basu yi tasiri ba

“Na gaji da cigaba da wannan auren. Nayi iya bakin ƙoƙarina wajen ganin na samu haihuwa amma duk ƙoƙarin nawa ya tashi a banza.” inji Ameh.

“Nabi tsarin ɗaukar ciki da haihuwa na musamman har sau biyu amma duk da haka ban samu nasara ba.” ta shaida ma kotu.

A wani labarin na daban kuma, sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin Ibrahim Traore sun fitar da sanarwar hanɓarar da gwamnatin shugaban ƙasa mai ci a yanzu wato Paul Henri Damiba wanda shima ya ƙwaci mulkin watanni takwas da suka gabata kamar yadda jaridar Vanguard ta wallafa.

Traore ya bayyana cewa sun samu nasarar hamɓarar da shugaban ne da haɗin gwuiwar sojojin da suka taimaka ma shugaba Damiba ƙwace mulki a watan Janairu waɗanda suka yi ƙorafin cewa ya gaza kawo ƙarshen matsalar yan ta’adda da ta addabi ƙasar.

An fitar da sanarwar ne a babban talabijin ɗin ƙasar wanda wani daga cikin jami’an sojojin ya karanta.

Lokacin da shugaban ƙasa Damiba ya karɓi mulki a watan Janairu, bayan kifar da shugaba Roch Kabore yayi alƙawarin samar da tsaro a ƙasar. Sai dai kuma matsaloli da dama sun cigaba ba da faruwa, haka nan ma rigingimu masu alaƙa da siyasa sun cigaba da ta’azzara.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe