32.4 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

Ina matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

IlimiIna matuƙar jin zafin yajin aikin da ASUU ke yi -Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace yana jin raɗaɗin zafin cigaba da yawaitar samun tsaikon da ɓangaren ilmin gaba da sakandire ke samu a ƙasar nan.

Haka kuma shugaba Buhari yayi kira ga ƙungiyar malaman jami’a ASUU da ta janye yajin aikin ta na wata bakwai, sannan a buɗe makarantu yayin da ake cigaba da tattaunawa don ganin an biya musu buƙatun da ba su fi ƙarfin gwamnati ba. Jaridar Vanguard ta rahoto.

Shugaba Buhari ya nuna takaicin sa

Shugaba Buhari yace:

Dole na bayyana cewa ina jin zafin ciwon yawaitar tsaikon da ake samu a ɓangaren jami’o’in mu, sannan ina yin amfani da wannan lokacin ranar murnar samun ƴancin kai, na sake maimaita kiran da nake yi ga ƙungiyar ASUU da su koma ajujuwa yayin da nake basu tabbacin magance matsalolin gwargwadon daidai ɗan abinda muke da shi.

Wannan gwamnatin tayi matuƙar ƙoƙari wurin magance waɗannan matsalolin waɗanda suka ƙi ci suka ƙi cinyewa na fiye da tsawon shekara sha ɗaya.

Gwamnatin tarayya zata cigaba da nemo kuɗaɗe daga ƙasashen waje da cikin gida domin samar da ilmi don tabbatar cewa ƴan ƙasa sun samu ilmi da ƙwarewa a fannin sana’o’i duba da muhimmancin da ilmi yake da shi wurin samar da cigaba da ayyukan yi.

A cikin Awa 24 kacal Peter Obi zai kawo karshen yajin aikin ASUU- cewar Mai magaba da yawun jam’iyyar

A wani labarin na daban kuma, mai magana da yawun jam’iyyar Labour Party ya bayyana cewa cikin sa’o’i uku kacal zai kawo ƙarshen yajin aikin ASUU.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Mista Peter Obi, zai kawo karshen duk wasu batutuwan da suka shafi yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) take yi idan har ya zama shugaban kasa. Yinusa Tanko, mai magana da yawun jam’iyyar ya ba da wannan tabbacin ne yayin da yake magana a gidan talabijin na Channels a ranar Alhamis, 29 ga watan satumba.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe