Sojojin ƙasar Burkina Faso bisa jagorancin kyaptin Ibrahim Traore sun fitar da sanarwar hanɓarar da gwamnatin shugaban ƙasa mai ci a yanzu wato Paul Henri Damiba wanda shima ya ƙwaci mulkin watanni takwas da suka gabata kamar yadda jaridar Vanguard ta wallafa.
Shugaban ƙasa ya gaza samar da tsaro a ƙasa
Traore ya bayyana cewa sun samu nasarar hamɓarar da shugaban ne da haɗin gwuiwar sojojin da suka taimaka ma shugaba Damiba ƙwace mulki a watan Janairu waɗanda dama suna ta yin ƙorafin cewa shugaban na yanzu ya gaza kawo ƙarshen matsalar yan ta’adda da ta addabi ƙasar wacce itace solar kifar da gwamnatin baya.
An fitar da sanarwar ne dai ranar juma’a a babban talabijin ɗin ƙasar wanda wani daga cikin jami’an sojojin da suka ƙaddamar da juyin mulkin ya karanta.
Lokacin da shugaban ƙasa Damiba ya karɓi mulki a watan Janairu, bayan kifar da shugaban ƙasa mai ci a wancan lokacin wato shugaba Roch Kabore, yayi alƙawarin samar da tsaro a ƙasar. Sai dai kuma matsaloli da dama sun cigaba ba da faruwa, haka nan ma rigingimu masu alaƙa da siyasa sun cigaba da ta’azzara a duk faɗin ƙasar ta Burkina faso.
Juyin mulkin dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban ƙasa Damiba ke dawowa daga taron majalissar ɗinkin duniya wanda ya gudana a birnin New York inda ya gabatar da jawaban da suka shafi ƙasar shi.
An rushe majalissun dokin ƙasar bayan kifar da shugaban ƙasa
Sojojin sun sanar da rushe duka majalissun dokokin ƙasar biyo bayan juyin mulkin. Sannan sun sanar da rufe iyakokin ƙasar tare da sanya dokar taƙaita zirga-zirga daga ƙarfe 09:00 na dare zuwa 05:00 na asuba a ƙasar baki ɗaya.
Gabanin hamɓarar da shugaban ƙasa Damiba, an tsinkayi sojojin na rurrufe manyan hanyoyin dake cikin babban birnin ƙasar Ouagadougou, tare da kuma dakatar Da watsa labarai a babban gidan talabijin ɗin ƙasar.
Da misalin ƙarfe huɗu na daren ranar juma’a ne dai mazauna birnin na Ougadougou suka rinƙa kiyo ƙarar harbe-harbe da kuma fashe-fashe musamman ma dai daga can yankin Kosyam, wanda anan ne fadar shugaban ƙasar take.
Amurka ta gargaɗi yan kasarta bayan hamɓarar da shugaban ƙasa
Ofishin jakadancin ƙasar Amurka ya gargaɗi ƴan ƙasar akan sun taƙaita zirga-zirga a cikin ƙasar sannan kuma su kasance suna bibiyar kafofin watsa labarai na cikin ƙasar.
A wani labarin na daban kuma, shugaban jam’iyyar APC, Abdulahi Adamu, ya zargi Bola Tinubu da yin watsi da yarjejeniyar da ta shafi kafa kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa (PCC).
Mista Adamu, a cikin wata wasika da ya aike wa Mista Tinubu, ya zargi Tinubu da yin watsi da kwamitin ayyuka na jam’iyyar.
Wannan dai shine sabon rikicin daya kunno kai a cikin jam’iyyar game da ‘yan kwamitin yaƙin neman zabe.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com