Wani zaƙaƙurin lauya ɗan Najeriya, Charles Osuji ya siya wani kamfani wanda a da yake koyon aiki a wurin.
Charles Osuji, wanda ke zaune a ƙasar Canada, ya garzaya LinkedIn inda ya nuna yadda sabon kamfanin nasa yake. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
Da yake bayar da labarin yadda abin ya fara, Osuji yace yana matsayin baƙo a Canada a lokacin, sannan yana neman wurin da zai koyi aiki a matsayin sa na ɗalibin zama lauya.
Ya samu dama bayan ya sha wahala
Yayi bayanin cewa wani lauya mai suna Smith ya bashi dama bayan ya nemi samun hakan a wurare da dama.
Yanzu haka ya siye kamfanin sannan ya sauya masa suna zuwa Osuji & Smith.
Osuji yace:
Tsohon maigida na Mr Smith ya bani damar ya ɗauke ni aiki. Tashi ɗaya, na karɓi damar, sannan na fara aiki, daga ƙarshe bayan shekara uku na siye kamfanin.
Yanzu haka, ya gina sabon ofishi. Ya nuna hotunan sabon ofishin nasa a LinkedIn inda yasa mutane da dama suka yaba matuƙa.
Kamfanin na sa na ƙara haɓɓaka
Tsohon wurin da nake zama yayi kaɗan ba zai iya ɗaukar haɓɓakar da kamfanin yayi ba, musamman kuɗirin da nake da shi na ganin na ba mutane da dama damar samun nasara, musamman mutanen da suke kama dani.
Saboda haka sai na gina sabon wuri mai ɗauke da ƙira ta zamani.
Makonni kaɗan da suka wuce, ni da ma’aikata na muka yi murnar cikar shekara biyar na kamfanin Osuji & Smith. Shekara biyar da suka wuce na siya kamfanin mai ma’aikata bakwai. Yanzu mun fi mu 24 sannan muna ƙara haɓɓaka.
Yadda ma’aikaci ya arce bayan kamfani yayi kuskuren biyan sa albashi har sau 330
A wani labarin na daban kuma, wani ma’aikaci ya cika wandonsa da iska bayan kamfani yayi kuskuren biyan sa albashi.
Wani ma’aikacin wata masana’anta a ƙasar Chile ya tsere bayan kamfanin yayi kuskuren biyan shi albashin sa sau 330.
Mutumin wanda ma’aikacin kamfanin Consorcio Industrial de Alimentos, an biya shi kimanin kuɗi £150,000 na aikin wata ɗaya, maimakon abinda yakamata a biya shi na £450 a matsayin albashin shi na watan Yuni
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com