Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, yaje birnin Landan ne domin ya huta, a cewar wani mamba na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasan, Ayo Oyalowo.
Rashin halartar Tinubu wurin rattaɓa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin ƴan takarar shugaban ƙasa ya janyo cece-kuce inda wasu ke yaɗa jita-jitar cewa ɗan takarar na jam’iyya mai mulki baya da lafiya. Jaridar Daily Trust ta rahoto.
Dalilin da yasa Tinubu ya tafi ƙasar waje
Amma da yake magana a wani shirin gidan talabijin na ARISE TV, Oyalowo yace:
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yana birnin Landan. Ba zai iya hutawa a Legas ba, ba za su bar shi ya huta ba. Mafi yawan lokuta yana zuwa Abuja, nan sun ƙi barin shi ya huta.
Wannan bawan Allah yana aikin aƙalla sa’o’i 20 cikin sa’o’i 24 kowace rana. Saboda haka mutane masu hankali suka ga ya dace ya bar ƙasa do mutane sun ƙi barin shi ya huta tunda yaƙin neman zaɓe na matsowa.
Takardar gayyatar zuwa wurin yarjejeniyar zaman lafiya ta iso ne bayan Tinubu ya bar ƙasa. Hatta mataimakin sa Sanata Kashim Shettima, baya gari, dole ya baro abinda yake yi a Maiduguri.
Saɓanin Atiku Abubakar, ɗan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), wanda ya sanar da tafiyar sa zuwa Dubai, mako guda kafin fara yaƙin neman zaɓe, ba a ji komai ba daga ƴan tawagar Tinubu, waɗanda ke sanar da shirye-shiryen abubuwan da zai yi.
Lokacin ƙarshe dai da rashin halartar Tinubu zuwa wurin wani taro ya haddasa cece-kuce shine lokacin da akayi taron ƙungiyar lauyoyi Nigerian Bar Association (NBA) a Legas.
Zaben 2023 :Shugaban jam’iyyar APC ya zargi Tinubu da saba alkawari a kan kwamitin yakin neman zabe
Shugaban jam’iyyar APC, Abdulahi Adamu, ya zargi Bola Tinubu da yin watsi da yarjejeniyar da ta shafi kafa kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa (PCC).
Mista Adamu, a cikin wata wasika da ya aike wa Mista Tinubu, ya zargi Tinubu da yin watsi da kwamitin ayyuka na jam’iyyar.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com