37.1 C
Abuja
Tuesday, March 28, 2023

Yadda ƴan ta’adda suka sanya ni sharɓar kuka -Shugaban majalisar dokokin Nasarawa

LabaraiYadda ƴan ta'adda suka sanya ni sharɓar kuka -Shugaban majalisar dokokin Nasarawa

Shugaban majalisar dokokin jihar Nasarawa, Alhajo Ibrahim Balarabe Abdullahi, ya bayyana yadda ƴan ta’addan Darul-Salam suka sanya shi sharɓar kuka.

Abdullahi, wanda yake wakiltar mazaɓun Ugya/Umaisha a jihar, ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai ziyarar jaje ga waɗanda ambaliyar ruwa ta ritsa da su.

Ƴan ta’addan sun muzgunawa mutanen yankin

Yace ayyukan ƴan ta’addan Darul-Salam sun kusan hana mutane bin hanyar Toto-Ugya-Umaisha, inda yace mutanen yankin sun samu sukuni bayan gwamnatin jihar ta kawo musu ɗauki.

Maganar gaskiya, abin ya kai lokacin da mutanen dake tafiye-tafiye a hanyar Toto-Ugya-Umaisha, suka dai na bi ta hanyar, saboda hare-haren ƴan ta’addan Darul-Salam amma dukkan godiya ta tabbata ga Allah domin yanzu mutane na sun samu sukuni.

A ranar da naji cewa ƴan ta’addan Darul-Salam sun mamaye mazaɓata, na sauko daga kan gadona na fara kuka. Daga bisani na fita nayi alwala sannan nayi sallar Nafila raka’a biyu.

Inji shi

Yayi wani muhimmin kira ga matasan yankin

Yayi kira ga mutanen mazaɓar sa da su goyi bayan gwamnatin jam’iyyar APC a ƙarƙashin jagorancin gwamna Abdullahi Sule, domin inganta tsaron rayuka da dukiyoyi a yankin.

Ya kuma nemi matasa da su zauna lafiya da bin doka da oda ga hukumomi musamman a lokutan yaƙin neman zaɓe.

Ƴan ta’adda sun halaka babban ɗa ga wani ɗan majalisa a jihar Bauchi

A wani labarin na daban kuma, ƴan ta’adda sun halaka babban ɗa ga wani ɗan majalisa a jihar Bauchi.

Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun halaka babban ɗa ga ɗan majalisar dake wakiltar mazaɓar Dass, Baba Ali, a majalisar dokokin jihar Bauchi.

Abdul Burra, kakakin shugaban majalisar Abubakar Suleiman, wanda ya gayawa wakilin jaridar The Punch yadda zaman majalisar ya kaya a ranar Talata, yace ɗan majalisar dake wakiltar mazaɓar Burra, Ado Wakili, shine ya bayyana hakan a zauren majalisar.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe