29 C
Abuja
Saturday, December 3, 2022

Edward Mordrake: Mutumin aka haifa da fuskar mace a keyarsa

LabaraiEdward Mordrake: Mutumin aka haifa da fuskar mace a keyarsa

An haifi Edward Mordrake ne a farkon karni na 19 da wata fuskar ta daban a keyarsa. Sai dai fuskar tasa ta keya bata gani, ko cin abinci ko kuma magana, Boingboing.net ta ruwaito.

Amma zai iya amfani da fuskar tasa wurin yin dariya, kuka ko kuma samar da wasu sautuka ba tare da Edward ya iya dakatarwa ba. Sai dai Edward ya bukaci likitoci su cire masa fuskar inda ya koka akan yadda cikin dare yake firgita sakamakon abubuwan da fuskar ke yi.

Ya halaka kansa lokacin yana da shekaru 23 ta hanyar shan guba saboda tsananin tsanar da ya yiwa halittarsa. Yana yawan bayyana yadda fuskar tasa ta keya ke murmushi a lokacin da yake cikin bacin rai, yayin da take kuka a lokacin da yake jindadi.

A lokacin rayuwarsa, a ko wanne dare yana kasa bacci saboda motsin da bakin fuskarsa ta keya ke yi ba tare da wani fitar sauti ba. Fuskar keyarsa ta wata kyakkyawar budurwa ce.

A lokacin rayuwarsa yana kin zuwa ziyara wurin ‘yan uwansa don gudun wani ya firgita ko kuma a tsokane shi.

Abokai 3 da aka haifa shekara daya, suka yi makaranta daya, suke zaune a gida daya, sun mutu an binne su a waje daya

Abokan su uku, ‘yan shekara 22 sun kasance kansu daya, inda suke gudanar da rayuwarsu a Al-Khobar, sun rasa rayukansu ne a wani hatsarin mota da ya rutsa da su. Sun kasance ‘yan asalin garin Damam ne.

  • Shafeeq:  Ya fito daga gundumar Malappuram ya kammala karatunsa wanda kafin mutuwarsa yana aiki ne tare da mahaifinsa mai suna Saidalavi Haji a wata cibiyar kasuwanci.
  • Ansif: Ya fito daga gundumar Wayanad, yana gaf da kammala karatunsa a Bahrain.
  • Sanad: Kuwa ya fito daga gundumar Kozhikode yana fafutukar komawa makaranta domin samun ilmi mai zurfi inda yake jiran a ɗage takunkumin tafiye-tafiye da aka kakaba saboda barkewar cutar Covid-19.

Makarantar su daya, ajin su daya, makwancin su na kabari ma daya

Sun yi karatunsu tare a International Indian School of Damam. Sun taso tare tun kuruciya har samartakar su tare ga shi kuma yanzu kabarurukansa manne da na juna.

Rahotanni sun bayyana cewa motar tasu ce ta rasa birki a hanyar da ke kan titin Damam Al Khobar wanda ke kusa da Dhahran. Inda Motar ta su ta bugi wasu motoci, ta dinga juyi akan titi sannan daga bisani ta kife, wanda hakan ne ya yi sanadiyar mutuwar su.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe