Wani dan shekara 16 ya rasu bayan biyawa kansa bukata sau 42 ba tare da ta hutawa ba a garin Rubiato da ke yankin Goias a kasar Brazil, Jaridar The Boshoston ta ruwaito.
Mahaifiyarsa ta sanar da manema labarai cewa ta san yadda dan ta ya saba da biyawa kansa bukata kuma tana da shirin kai shi asibiti don ganin likita, ashe ta yi latti.
Matashin ya fara biyawa kansa bukata tun tsakiyar dare inda ya kwashe awoyi da dama yana abu guda. A makaranta, ‘yan ajinsu sun bayyana yadda yaron ke da matsala.
Sun bayyana yadda yake tsananin sha’awar mata ba tare da ya damu da shekarunsu, halitta, kyau ko kalar fatarsu ba. A dakinsa, an ga hotuna da bidiyoyi da dama na tsiraicin mata wadanda ya adana a na’urarsa mai kwakwalwa.
Ta yuwu ya rasu ne bayan ruwan jikinsa da kuma karfinsa duk sun kare saboda yadda ya dinga biyan bukatar kansa har sau 42.
An cafke tsoho mai shekara 84 ya yiwa ƴar shekara 8 fyaɗe
Hukumar ƴan sandan jihar Ogun tace ta cafke wani tsoho mai suna Stephen Jack, mai shekara 84 a duniya bisa zargin aikata fyade kan yarinya ƴar shekara 8 a jihar.
A cewar ƴan sandan, an cafke tsohon ne bayan mahaifin yarinyar ya kai rahoton lamarin a ofishin ƴan sanda. Jaridar The Cable ta rahoto.
Mahaifin yarinyar ya garzaya ofishin ƴan sandan ne bayan ya lura cewa yarinyar sa na zubar da jini a gabanta, sannan tace tsohon ne yayi mata fƴaɗe.
A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Asabar, kakakin hukumar ƴan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, yace binciken farko da akayi ya nuna cewa tsohon yayi ƙaurin suna wurin lalata ƙananan yara a unguwar Okun Owa, a Ijebu Ode.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com