
FCT, Abuja – Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Mista Peter Obi, zai kawo karshen duk wasu batutuwan da suka shafi yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) take yi idan har ya zama shugaban kasa. Yinusa Tanko, mai magana da yawun jam’iyyar ya ba da wannan tabbacin ne yayin da yake magana a gidan talabijin na Channels a ranar Alhamis, 29 ga watan satumba.
Ga abinda ya ce: “Ina tabbatar muku cewa yajin aikin da ASUU ta ke yi dama saura hukumomi dake yajin aiki idan har peter Obi ya ci zabe cikin Awa 24 zai kawo karshen matsalar.
Tanko ya kara da cewa dan takarar yana shirin yadda zai mayar da Najeriya kasa mai albarka.
Yace: “Ya cw peter Obi yana ma garin Niger kallon kasar Netherlands kuma ya ce jihar ita kadai za ta iya ci gaba da samar da kayayyaki da kadarorin da za a iya amfani da su wajen sauya yanayin tattalin arzikin kasar nan. ”
ASUU :Kotu ta umurci ASUU data janye yajin aiki
A yau Laraba ne kotun masana’antu ta Najeriya ta umarci kungiyar malaman jami’o’i da ta janye yajin aikin da ta shafe watanni tana yi a fadin kasar nan.
Jaridar PUNCH ta rahoto cewa ASUU ta tsunduma yajin aiki tun ranar 14 ga watan Fabrairu domin neman a biya su hakkokin su da suka hada da inganta jami’o’i, nazarin albashin malaman jami’o’i da dai sauransu.
An yi ta zaman ganawa tsakanin gwamnati da Mambobin kungiyar ta ASUU sai dai har yanzu an kasa cimma matsaya.
Sakamakon haka gwamnatin tarayya ta garzaya kotu domin kalubalantar yajin aikin.
Kamar yadda shafin jaridar TheCable ya ruwaito, gwamnatin ta bakin lauyanta, James Igwe, ya roki kotun da ta dakatar da ASUU daga cigaba da yajin aikin, har zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan karar.
Cikakkun bayanai daga baya…
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com