Wani rahoto ya bayyana yadda mai ba wa fulawa ruwa a gidan wani attajiri da ke Kenya ya dirka wa ‘yan mata uku ‘yan gida daya ciki, Legit.ng ta ruwaito.
Tsohon dan majalisa, Shehu Sani ya wallafa wannan labari a shafinsa na Facebook wanda Legit.ng ta gani.
A cewarsa, duk da yadda iyayen ‘yan matan uku ke da tsanani inda su ke yawan rufe su a gida ba tare da barinsu su yi tarayya da kawaye ba, sai ga shi mai ba fulawa ruwa a gidan ya yi musu ciki.
An samu bayanai akan cewa mutumin ne kadai wanda ake bari yana shiga gidan har yake iya harka da su.
Sai dai ashe akwai wata harkalla da ke shiga tsakaninsa da ‘yan matan inda yake lalata da duk ukun ba tare da sanin iyayensu masu tsananin addini ba.
Bayan samun labarin hakan, iyayensu sun yi matukar mamaki akan yadda hakan ya faru duk da yadda suke iyakar kokarin su akan yaran.
Yayin da aka titsiye su don jin wanda yayi musu ciki, sun sanar da su cewa mai ba fulawa ruwa ne. Hakan yasa mahaifiyarsu ta yanke jiki ta fadi kasa.
An samu bayanin yadda su ka fara lalata da shi gabadayansu ne bayan babbar ta kama ta biyun su na masha’ar. Daga nan ne ta bukaci itama ya biya mata bukatarta don ta rufa masa asiri.
Yayin da suke tsaka da lalata Riga kuma ta ukun ta kama su, itama ta nemi yayi lalatar da ita don ta rufa musu asiri.
Bayan daukar lokaci mai tsawo ana hakan, sai duk su ka samu ciki. A yanzu haka sun riga sun haihu. Kuma haka nan iyayen su ka yi hakuri bayan zurfafa tunanin saboda tsananin su ne hakan ya faru.
Iyayen sun kore shi daga aiki amma har yanzu ‘yan matan na tura masa kudi, su na kuma son sa a matsayin uban yaransu mata biyu da namiji daya.
A gado daya muke kwana: Yadda tagwaye su ka dirka wa mace daya ciki, tana gab da haihuwa
Wasu tagwaye sun janyo cece-kuce bayan sun bayyana yadda su ke kwanciya da mace daya kuma yanzu haka su na shirin tarbar jaririnsu don ta kusa haihuwa, Legit.ng ta ruwaito.
A gado daya su ke kwana kullum kamar yadda su ka bayyana. Kuma wannan lamarin ne yafi bai wa kowa mamaki.
A wani bidiyo da Nicholas Kioko ya saki a shafinsa ba Youtube, tagwayen sun bayyana irin rayuwar soyayyar da su ke yi da matarsu.
Teddy da Peter sun bayyana cewa su na gab da zama iyaye kuma ba su riga sun yi aure ba tukunna amma su na kiranta da matarsu.
Kamar yadda Teddy yace:
“Mu da matarmu ne muka zama. Kuma mun yanke shawarar aurenta ne kasancewar mu tagwaye. Yanzu haka a daki daya muke kwana.”
Sun bayyana yadda su ka hadu a coci wanda daga nan ne su ka yi musayar lambar waya da ita.
Dama Kuma Peter ba ya da waya a lokacin don haka yana amfani da wayar dan uwansa ne.
Yayin da aka tambayeta ko cikin wanene a jikinta, ta ce bata sani ba, hakan yasa su biyun su ka amince dan ya zama nasu.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com