27.5 C
Abuja
Wednesday, March 22, 2023

Yadda rigima ta ɓarke tsakanin Sowore da Ƙashim Shettima a wurin rattaɓa hannu kan zaman lafiya

LabaraiYadda rigima ta ɓarke tsakanin Sowore da Ƙashim Shettima a wurin rattaɓa hannu kan zaman lafiya

An samu hargitsi tsakanin Kashim Shettima da Omoyele Sowore a wurin rattaɓa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a tsakanin ƴan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyu daban-daban da za su fafata a babban zaɓen 2023 dake tafe.

Taron wanda aka yi a ɗakin taron ƙasa da ƙasa (ICC) a Abuja ranar Alhamis, 29 ga watan Satumba, wanda kwamitin zaman lafiya na ƙasa ya shirya sannan ya samu halartar kusan dukkanin ƴan takara na jam’iyyu face Asiwaju Bola Tinubu na jam’iyyar APC. Jaridar Legit.ng ta rahoto.

Yadda rigimar ta samo asali tsakanin Kashim Shettima da Sowore

Sai dai, rigima ta ɓarke a wurin taron lokacin da aka ba Sowore ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC wajen zama a bayan Kashim Shettima, tsohon gwamnan jihar Borno kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na APC.

Shettima yana a wurin taron ne domin wakiltar Bola Tinubu, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC.

Jin haushin hukuncin da masu shirya taron suka yanke na barin Shettima, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na APC,
ya zauna a sahun farko inda ƴan takarar shugaban ƙasa ke zaune, sai kawai Sowore ya fara zazzaga wa tsohon gwamnan na Borno kalamai.

Da wasu daga cikin mahalarta taron suka buƙace shi da ya haƙura, sai Sowore yace zai cigaba da abinda yake yi domin saboda kishin ƙasa yake yi.

A kalaman sa:

Hakan ba yana nufin ba zan cigaba da faɗar ko cigaba da matsaya ta ba, matsaya iri daya ce muke da ita ta zama a sahun gaba. Na tunkare shi sannan na tambaye sa meyasa yake zaune a nan bayan Tinubu baya nan.

Da ace ina zaune a wurin, ba zan tashi domin sa ba sabodaTinubu shine yakamata ya zauna a wajen ba shi ba. Ba zaka iya nemin mulkin Najeriya a ɓoye ba.

Kashe kala: Kashim Shettima na shan zolaya a Twitter akan wankan da ya dauka zuwa taron NBA

A wani labarin na daban kuma, ƴan Najeriya sun zolayi Kashim Shettima a Twitter kan wankan da 6a ɗauka zuwa taron NBA.

Ƙashim Shettima na shan zolaya a Twitter bayan ya dauki wani wanka yayin da yaje taron Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya, NBA a ranar 22 ga watan Augustan 2022 a Jihar Legas, LIB ta ruwaito.

Shi ne dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC tare da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe