Biyo bayan ƙara yawan kuɗin ruwa zuwa kaso 15.5% da babban bankin Najeriya (CBN), yayi, bankin ya umurci bankuna da riƙa biyan kaso 4.65% na kuɗin ruwa kan asusunan ajiya na banki, hakan yasa an samo ƙarin kaso 4.2% kan wanda bankunan ke biya a baya.
Wannan umurnin na zuwa ne bisa ƙarin da akayi na tsarin farashin kuɗi zuwa kaso 15.5% daga kaso 14%. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
Gwamnan babban bankin, Godwin Emefiele, shine ya sanar da sauye-sauyen ranar Talata 27 ga watan Satumban 2022.
Yadda sabon tsarin yake
Tsarin farashin kuɗi (MPR) shine farashin da babban bankin Najeriya ke ba bankuna rancen kuɗaɗe. Shine mahangar da ake dubawa wurin bayar da rance masana’antar kuɗi.
Farashin kuɗaɗen ajiya shine farashin da bankuna ke biyan kwastomomin su domin ajiyar kuɗi a bankunan su.
Da farko dai babban bankin Najeriya ya bar MPR a kaso 14%, hakan na nufin an samu ƙarin kaso 30% daga kaso 4.2%.
Wannan ƙarin na kuɗin ruwa kan asusunan ajiya zai bunƙasa ajiya sannan ya zama wani hanyar magance hauhawan farashi
Masu zuba jari na asarar kuɗaɗe idan hauhawan farashi ya zarce kuɗin ruwan da ake samu a asusunan ajiya, saboda hauhawan farashi yana cinye ƙarfin siyan kayayyaki da kwastomomi ke da shi.
Masu sharhi kan lamura na ganin cewa wannan ƙarin na kuɗin ruwa da babban bankin Najeriya yayi, zai daƙiƙe hauhawan farashi wanda yanzu haka yakai kaso 20.52% wanda ba a taɓa samu ba cikin shekara 17.
Cikin wata 3: ‘Yan Najeriya sun kashe sama da N100b domin neman ilimi a kasashen ketare – CBN
A wani labarin na daban kuma, babban bankin Najeriya yace ƴan Najeriya sun kashe sama da N1o0bn domin neman ilmi a ƙasashen waje.
A wani bayani da Babban Bankin Najeriya wato CBN ta fitar, ta bayyana cewa ƴan Najeriya sun kashe abƙalla dala miliyan 220.86 kan neman ilimi a kasar waje daga watan Disambar 2021 zuwa Fabrairun 2022.
Hakan na nufin an kashe sama da naira biliyan 100 a kiyasin kuɗin Najeriya. Hakan ya faru ne saboda gibi da bangaren ilimi musamman na jami’o’i Najeriya suke fuskanta.
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com