Wata lauya ‘yar Najeriya ta musanta batutuwan jama’a wanda su ke cewa ai masu kudi ba su da kwanciyar hankali kamar yadda LIB ta ruwaito.
A wata wallafa wacce tayi a Twitter wacce jama’a su ka dinga yadawa, @nwaoma007 ta musanta yadda mutane da dama ke cewa ai masu kudi ba su da kwanciyar hankali.
A cewarta:
“Na tsani yin surutai. Amma masu kudi da yawa su na kwanciyar hankali da farinciki mai yawa. Yaransu su na morewa.
“Ba sa shaye-shaye kuma su na samun daukaka. Kuma su na zaune cikin kwanciyar hankali da masoyansu ba fiye da yadda talakawa ke fama. Yaudarar kai ku ke yi idan ku na kallonsu a akasin hakan.”
Kullum garin kwaki nake ci, don haka zan fi fahimtar matsalolin talakawa, Amaechi
Rotimi Amaechi, mai neman kujerar shugaban karkashin jami’iyyar APC sannan tsohon ministan sufurin ya ce yafi kowanne ‘dan takara cancanta, duba da asalinsa talaka ne tilis, The Punch ta ruwaito.
Ya fadi hakanne yayin tattaunawa da wakilan jam’iyyar APC a jihar Neja, saboda yadda zaben fidda gwani na karatowa.
A cewarsa sai ya fi saukin cudanya da talakawa saboda tuntuni a kowacce rana yana shan garin kwaki sau uku, kuma har yanzu bai dena ba.
Tsohon ministan ya bayyana yadda duk da irin gogewar da ya yi a baya wacce ya rike mukamai kamar; kakakin majalisa, gwamna, minista da kuma darakta-janar na kamfen din shugaban kasa har sau biyu, amma ya matukar bambanta da sauran ‘yan takarkari saboda shi mutumin mutane ne.
Ya bayyana yadda iyayensa suka kasance marasa hannu da shuni.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausaagmail-com