34.9 C
Abuja
Monday, March 20, 2023

Ummita: Kotu ta sanya ranar sauraron ƙarar da ake yiwa ɗan ƙasar Chana

LabaraiUmmita: Kotu ta sanya ranar sauraron ƙarar da ake yiwa ɗan ƙasar Chana

Wata babbar kotun jihar Kano wacce mai shari’a Sanusi Ado Ma’aji ke jagoranta, ta ɗaga sauraron ƙarar da ake yiwa ɗan ƙasar Chana, Geng Quangrong, wanda ake tuhuma da kisan masoyiyar sa, Ummulkulsum Sani Buhari wacce aka fi sani da suna Ummita.

Alƙalin ya ɗaga sauraron ƙarar ne bisa rashin halartar lauyan dake kare wanda aƙe tuhumar. Jaridar Daily Trust ta rahoto.

Ya nemi kotun da ta bashi damar samo lauya

A yayin da aka cigaba da saurarin ƙarar a ranar Alhamis, Geng Quangrong ya roƙi kotun da ta ɗaga sauraron ƙarar domin ya samu damar tuntuɓar lauyan sa domin wakiltar sa.

Da yake mayar da martani, Antoni janar na jihar Kano, Musa Abdullahi Lawan, bai nuna ƙin amincewa da buƙatar wanda ake ƙara ba ta a ɗaga sauraron shari’ar.

Lauyan gwamnatin yace:

Tabbas ba zamu iya cigaba da wannan shari’ar ba babu lauya, mai kare wanda ake ƙara. Wannan shine tsarin. A bisa halin da ake ciki, mun nemi da a ɗaga sauraron ƙarar na ɗan gajeran lokaci domin bada dama ga wanda ake ƙara ya samo lauya.

Mai shari’a Sanusi Ado Ma’aji ya ɗaga sauraron ƙarar sai zuwa ranar 4 ga watan Oktoban 2022.

Laifukan da ake tuhumar ɗan ƙasar Chana da su

Ana dai tuhumar Geng da laifin keta iyaka da kuma halaka Ummulkulthum Buhari (Ummita) mai shekaru 23 da haihuwa a duniya.

Mamaciyar da wanda ake tuhumar dai soyayya suke yi a tsakanin su kafin dangantakar ta su tayi tsami.

Yadda ɗan Chana ya yaudari Ummita cewa ya musulunta -Babbar ƙawarta

A wani labarin na daban kuma, wata babbar ƙawar Ummita ta bayyana yadda ɗan Chama ya yaudari ƙawarta cewa ya musulunta.

Wata ƙawar Ummukulsum Sani Buhari (Ummita) matashiyar nan da Geng Quanrong ya halaka a Kano, ta bayyana cewa ya yaudari marigayiyar da cewa ya musulunta domin ta aure shi.

Daily Trust ta rahoto cewa Quanrong yanzu haka yana garƙame a hannun ƴan sanda bisa halaka Ummita a gidan iyayenta a ranar Juma’a. Ummita da Quanrong masoya ne.

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayoyin ku a wajen sharhi dake kasa.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Facebook Page

Twitter Page

Telegram Channel

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: info@labarunhausa.com

Ku duba wasu labaran mu

Check out other tags:

Labaran da suka fi tashe