
Shugaban jam’iyyar APC, Abdulahi Adamu, ya zargi Bola Tinubu da yin watsi da yarjejeniyar da ta shafi kafa kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa (PCC).
Mista Adamu, a cikin wata wasika da ya aike wa Mista Tinubu, ya zargi Tinubu da yin watsi da kwamitin ayyuka na jam’iyyar.
Wannan itace sabuwar rikicin data kunno kai a cikin jam’iyyar game da ‘yan kwamitin yakin neman zabe. Jaridar Allnews ta ruwaito yadda gwamnoni suka yi barazanar yin zagon kasa ga yakin neman zaben shugaban kasa kan sunayen da aka fitar.
Rashin amincewar gwamnonin shi ya tilasta aka dage ranar taron kaddamar da ‘yan kwamitin har zuwa nan da wani lokaci.
Ko da yake, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta dage dokar data saka na hana yakin neman zabe a ranar Laraba, sai dai har yanzu jam’iyya mai mulki ba ta fara yakin neman zaben ta ba, kasancewar Mista Tinubu baya kasar.
Mista Adamu, a cikin wasikar da aka fitar,ya ce kwamitin ayyuka na jam’iyyar ta yi nadamar samun wannan labari. Inda ya kara da cewa Tinubu ya yi alkawarin haɗa kai da kwamitin ayyuka na jam’iyyar.
Duk da cewa Tinubu da Adamu sun yi watsi da rade-radin cewa akwai baraka a baya, amma akwai rahotannin cewa akwai ‘yar tsama tsakanin su.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye: hello@labarunhausaagmail-com